Bidiyon Halilu Sabubu na Karshe da Yake Rokon Bello Turji, Ya Tura Sako ga Malamai

Bidiyon Halilu Sabubu na Karshe da Yake Rokon Bello Turji, Ya Tura Sako ga Malamai

  • An wallafa faifan bidiyo inda marigayi dan ta'adda, Halilu Sabubu ya ke rokon yan uwansa kan lamarin tsaro
  • Sabubu ya kira manyan yan bindiga da suka hada da Bello Turji da Alhaji Ado da Alhaji Shingi domin shawo karshen lamarin
  • Sabubu ya wallafa bidiyon ne a ranar Talata 10 ga watan Satumbar 2024 kwanaki uku kafin sojoji su hallaka shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Kasurgumin dan ta'adda, Halilu Sabubu ya rasa ransa a hannun sojojin Najeriya.

Sabubu wanda aka tabbatar shi ne mai gidan Bello Turji ya rasa ransa da safiyar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024.

An gano inda Halilu Sabubu ke rokon yan ta'adda a bidiyonsa na karshe
A cikin bidiyonsa na karshe, Halilu Sabubu ya roki samun zaman lafiya. Hoto: @zagazolamakama/@HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Bidiyon Halilu Sabubu yana rokon yan ta'adda

Kara karanta wannan

Halilu Buzu: Yadda mugun ‘dan bindiga ya gamu da ajali da ya fada tarkon sojoji

Shafin Zagazola Makama ya wallafa bidiyon karshe da Sabubu ya yi kafin hallaka shi a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon an gano yadda kasurgumin dan ta'addan ke rokon Fulani yan uwansa kan kashe-kashe.

Sabubu ya kira sunayen manyan yan ta'adda ciki har da Bello Turji game da kawo karshen kashe-kashe.

Bidiyon Halilu Sabubu na karshe a duniya

"Ina rokonku dukanku mu tsaya mu kwatawa Fulani yancinsu, ba na ce a bar sata ba amma mu bar kashe kanmu da kanmu a bar yiwa Fulani sata."
"Ina kira a Katsina da Zamfara da Kebbi da Kaduna da Niger a bar yiwa Fulani sata, mu tsaya tsayin daka wurin koyi da wasu ƙasashe da ba a yiwa Fulani sata."
"Ni Sabubu na roka a bar wa Fulani sata, rigimar mu ta tsaya ga jami'an tsaro da yan sa-kai, mu ragawa wanda ya bimu ko garin da suka bimu."

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe mai gidan Bello Turji da wasu jiga jigan yan ta'adda

- Halilu Sabubu

Sabubu ya roki malamai addu'ar zaman lafiya

Daga cikin wadanda ya kira akwai Alhaji Ado da Alhaji Shingi da Alhaji Nashamada Dogo Gide.

Sauran sun hada da Gwaska da Black inda ya ce su kadai ya ke sauraren a yanzu inda ya ce a yi zama domin raga ma dangi.

Sabubu ya roki malaman addini da su yi ta addu'ar samun zaman lafiya madadin cewa a yi kaza da kaza.

Ya ce da ace gwamnati tana da niyyar kawo karshen rashin tsaro da ta dade da yin haka.

Bello Turji ya sake sabon bidiyo

Kun ji cewa dan ta'adda, Bello Turji ya gargadi lauya, Bulama Bukarti kan rahoton da ya fitar game da kakaba haraji a Moriki.

Turji ya ce ya kamata lauyan ya nemi bayanai ta kowane bangare kafin yin adalci kan lamarin ba tare da nuna wariya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.