Najeriya da Sauran Kasashe 10 da Suka Runtumo Bashin $140bn a Bankin Duniya
- Wasu kasashe musamman daga nahiyar Asiya da Afrika sun karbo bashin kudi masu yawa daga bankin duniya
- Kasashe kusan 10 sun ci bashin abin da ya kusa kai $150bn daga babban bankin saboda dalilan tattalin arziki
- Kasar Vietnam ta saba rugawa neman taimako wajen bankin duniya, ta taba karbo aron $500m a lokaci guda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Najeriya ta yi suna wajen karbo aron kudi kasashe da kamfanonin duniya, har wani lokacin a kan yafe mata bashin.
Gwamnatin Najeriya ta ganewa zuwa bankin duniya ta karbo aron kudi duk da wasu su na gargadi a kan lafto bashi daga ketare.
Najeriya da karbo bashi a bankin duniya
Alkaluman da aka samu daga shafin Stati Sense da ke dandalin X ya tabbatar da matsayin Najeriya wajen cin bashin bankin duniya.
Najeriya ce ta uku a jerin kasashen da babban bankin duniya yake bin bashin kudi a yau.
A lissafin canjin kudi a yau, bashin da bankin na duniya yake bin Najeriya ya zarce Naira tiriliyan 25 domin dala biliyan 16 ne.
Kasashen da suka tara bashin bankin duniya
Sauran kasashen da ke kan gaba wajen karbo irin wannan bashi su ne Bangladesh da Fakistan wadanda su ke a nahiyar Asiya.
FDI Intelligence ta ce rabin kasashe sun ci bashin bankin Duniya. Indiya da ta karbo bashin kusan $16bn ta na cikin sahun gaba.
Vietnam ta ci bashin $12.0bn daga bankin domin inganta tattalin arziki. Ko bayan annobar COVID-19, kasar ta karbo aron $220m.
Ragowar kasashen da ke neman mafaka a bankin duk sun fito ne daga nahiyar Afrika.
Kasashen sun hada da Kenya, Tanzaniya da Uganda da ke gabashin Afrika sai kuma kasar Ghana da ta ke yankin Afrika ta yamma.
1. Bangladesh - $20.5bn
2. Fakistan - $17.9bn
3. Najeriya - $16.5bn
4. Indiya - $15.9bn
5. Ethiopia - $12.2bn
6. Kenya - $12.0bn
7. Vietnam - $12.0bn
8. Tanzaniya - $11.7bn
9. Ghana - $6.7bn
10. Uganda - $4.8bn
SERAP na maganar bashin bankin Duniya
A baya an ji labari cewa kungiyar SERAP na son a binciki gwamnonin jihohi kan bashi da aka karbo domin rage raɗadin talauci.
SERAP ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ta hannun Lateef Fagbemi (SAN) ya binciki bashin $1.5bn da suka karɓo daga hannun bankin.
Asali: Legit.ng