Ambaliya: Gwamnatin Tarayya, Dangote, Dantata da Wadanda Su ka ba Borno Tallafi
- Gwamnatin tarayya ta ba da Naira biliyan uku ga jihar Borno a sakamakon ambaliyar ruwan da ta barke
- Mai kudin Najeriya da Afrika ya ba hukumar NEMA tallafin N1.5bn ta hannunsa da kuma gidauniyar Aliko Dangote
- Gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar tarayya sun aiko da gudumuwa kuma ana sa ran wasu za su cigaba da aikowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Borno - A sakamakon ambaliyar ruwan da ta rutsa da Maiduguri a jihar Borno, ana cigaba da taimakawa gwamnati da tallafi.
Rahoton nan ya yi kokarin tattaro attajirai, gwamnatoci da ‘yan siyasar da suka ba da gudumuwa domin taimakawa jihar Borno.
Tallafin ambaliya a jihar Borno
1. Gwamnatin tarayya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya na faruwa sai aka ji gwamnatin tarayya ta aikowa jihar Borno N3bn domin magance matsalar da jama’a suka shiga.
Tribune ta rahoto gwamna Babagana Zulum ya na wannan bayani lokacin da ya ziyarci wani sansanin da aka yi wa ‘yan gudun hijira.
2. Aliko Dangote
Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya ce hukumar NEMA ta nemi ya kawo tallafi, saboda haka aka amince a ba da gudumuwar N1bn.
Bayan nan kuma gidauniyar ‘dan kasuwan ta kara da N500m kamar yadda labarin ya zo a jaridar The Cable a yammacin ranar Juma’a.
3. Jihar Adamawa
A madadin gwamnatin Adamawa, mai girma Ahmadu Umar Fintiri ya ba da gudumuwar N50m a matsayin gudumuwar ambaliya.
Baya ga kudi, an rahoto cewa gwamnan jihar Adamawa ya ba jihar kyautar jiragen ruwa.
4. Jihar Gombe
Gwamnati da mutanen Gombe sun ba da gudumuwar kudi har N100m domin a taimaki bayin Allah da ambaliya ta shafa a Maiduguri.
Jaridar Punch ta ce mataimakin gwamnan jihar Gombe ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi wa mutanen Borno Allah kyauta.
5. Jihar Nasarawa
Rahoto ya gabata cewa gwamna Abdullahi Sule ya sanar da cewa ya aiko da motocin kayan abinci domin a taimakawa gwamnatin Borno.
Mai girma gwamnan Nasarawa bai fadi adadin motocin abincin da ya aikowa jama’a ba.
6. Hon. Mukhtar Betara
Baya an ji cewa ‘dan majalisar wakilan tarayya, Mukhtar Betara ya taimaka da gudumuwar N10m bayan jin labarin wannan ambaliyar.
Hon. Betara mai wakiltar mutanen Biu/Bayo/Shani and Kwaya Kusar yana sa ran kudin zai rage radadin da mutanen jiharsa suka shiga.
7. Atiku Abubakar
Daily Trust ta ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ba gwamnatin Borno gudumuwar N100m a ranar Lahadi.
8. Gwamnatin Kano
Gwamnatin Kano ta ba da tallafin N100m a sanadiyyar ambaliyar. Wasu kwamishononin Abba Kabir Yusuf suka sanar da haka.
9. Aminu Dantata
A ranar Talata aka samu labari cewa Alhaji Aminu Dantata, ya ba da tallafin Naira biliyan 1.5 ga mutanen da ambaliya ta shafa a Borno.
10. Sanatoci
‘Yan majalisar dattawa sun ziyarci gidan gwamnatin jihar Borno domin jajanta wa jama'ar Maiduguri, suka ba da tallafin N74m.
11. 'Yan majalisar wakilai
Bayan sanatoci, ‘yan majalisar wakilan tarayya sun yi karo-karo inda aka rahoto cewa sun hadawa mutanen Maiduguri gudumuwar N100m.
12. Peter Obi
‘Dan takaran shugaban kasa a karkashin LP a zaben 2023, Peter Obi ya ba da N50m ga mutanen Maiduguri kamar yadda Punch ta rahoto.
13. Remi Tinubu
Uwargidar Najeriya kuma mai dakin shugaban kasa, Remi Tinubu ta warewa mutanen da ambaliyar ya shafa N500m a makon nan.
Sauran wadanda suka ba Borno gudumuwa
Aminiya ta ce sauran wadanda suka ba da gudumuwa sun hada da Hon. Zainab Gimba, Ibrahim Umar, Zakari Dikwa, Abubakar Maifata.
Sannan akwai ‘yan majalisa da-dama daga Borno, sauran ‘yan siyasa, mawaka kamar Dauda Kahutu (Rarara), kungiyoyi da kamfanoni.
Gwamnatocin jihohi da yawa sun ba da makudan miliyoyi domin taimakawa Borno.
9. Aminu Dantata
An fara samun saukin ambaliyar Borno
A baya an samu labari ruwan da mamaye Maiduguri ya fara janyewa bayan mutane sun yi kwana da kwanaki a yanayi mai ban tausayi.
Jami'an hukumar SEMA da sauran jama'a na bada agajin gaggawa kuma zuwa yammacin Alhamis, mutane 3,682 aka ceto a Borno.
Asali: Legit.ng