Halilu Buzu: Yadda Mugun ‘Dan Bindiga Ya Gamu da Ajali da Ya Fada Tarkon Sojoji

Halilu Buzu: Yadda Mugun ‘Dan Bindiga Ya Gamu da Ajali da Ya Fada Tarkon Sojoji

  • Ta’adin Halilu Sabubu Buzu ya zo karshe domin sojoji sun hallaka shi a wata gwabzawa da aka yi a cikin jeji
  • Dakarun sojoji sun yi kwantan bauna a wani kauye, ta haka su ka hallaka Sububu da yaransa a jihar Zamfara
  • Bayanai sun bayyana cewa yaran Halilu Buzu da yawa sun hallaka, kuma jami’ai sun karbe kayan yakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Zamfara - Bayanai sun cigaba da fitowa game da mutuwar hatsabibin ‘dan bindigar nan Halilu Sububu da aka fi sani da Buzu.

Kafin mutuwarsa a hannun dakarun sojojin kasar Najeriya, Halilu Sububu ya fitini al’ummar Zamfara da jihohin kewayenta.

Halilu Sububu Buzu
Sojoji sun kashe Halilu Sububu Buzu da mayakansa a Zamfara Hoto: @zagazolamakama/@HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Yadda aka kashe Halilu Sububu Buzu

A wani rahoto na Daily Trust, an bayyana yadda shi wannan ‘dan bindiga ya gamu da ajalinsa a yammacin Alhamis da ta wuce.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe mai gidan Bello Turji da wasu jiga jigan yan ta'adda

An harbe Halilu Sububu da wasu mayakansa ne yayin arba da dakarun Operation Hadarin Daji da ke kokarin magance rashin tsaro.

Wata majiya ta ce sojojin Najeriya sun hallaka ‘dan ta’addan ne a wani kwantan bauna da aka yi masu a yankin Kwaren-Kirya.

‘Yan ta’addan sun yi arangama da jami’an tsaro ne a wannan kauye da ke kan hanyar Mayanchi zuwa garin Mafara a jihar Zamfara.

Mutuwar Halilu Sububu Buzu da yaransa

"Mun fahimci ‘yan bindigan su na kokarin tsallake wani kududdufi ne lokacin da dakarun da suka yi masu kwantan-bauna suka duran masu
"Sai suka kasha Sububu da mayakansa
"Mun ji cewa baburan ‘yan bindiga uku kacal su ka tsira daga harin a lokacin da aka yi arangamar."

- Wata majiya

"Daga Buzu sai yaronsa Bello Turji"

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

Majiyar ta ce sojoji sun yi nasarar karbe babura da makaman wadannan fitinannan miyagu yayin da jama’a ke ta murna a Zamfara.

Baya ga Buzu wanda asalinsa mutumin Nijar ne da ya tare a Najeriya ya na hakar gwal a garin Bagega, ana sa ran cafke Bello Turji.

Tun a watannin baya aka ji jami’an sojojin kasa su na cigiyar Halilu Buzu. Zagazola Makama ya bayyana lamarin da nakasu ga miyagu.

Malami ya koka da azzaluman shugabanni

Rahoto ya gabata a kan yadda Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid ya ji haushin yadda kwatsam aka ji litar man fetur ya doshi N1, 000.

Ganin yadda ake fama da rayuwar kunci da rashin aminci, Malamin ya na so Allah SWT ya casa azzaluman masu mulki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng