Mai Garkuwa da Mutane Ya Yanke Sassan Jikin Budurwa bayan Karbar Kudin Fansa

Mai Garkuwa da Mutane Ya Yanke Sassan Jikin Budurwa bayan Karbar Kudin Fansa

  • Rundunar yan sandan Kogi ta tabbatar da cafke wani matashi da ya yi garkuwa da wata daliba mai shekaru 19 kuma ya kashe ta
  • Mai garkuwa da mutanen dan shekaru 20 mai suna Paul Jeremiah ya kashe dalibar ne bayan an biya shi kudin fansa da ya nema
  • Rundunar yan sanda ta bayyana cewa Paul Jeremiah ya cire wasu sassan jikin budurwar kafin ya toni rami ya birne gawarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Yan sanda a jihar Kogi sun yi nasarar cafke wani matashi da ake zargi da garkuwa da wata dalibar makaranta.

Ana zargin matashin mai suna Paul Jeremiah da sace wata daliba budurwa mai shekaru 19 da kuma kashe ta har lahira.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da akidar Boko Haram sun shigo Sakkwato daga kasar waje sun kafa daula

jihar Kogi
An kama mai garkuwa da ya kashe budurwa a Kogi. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa dalibar na karatu ne a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi.

An kama wanda ya 'kashe' budurwa a Kogi

Kakakin yan sanda a jihar Kogi, SP William Aya ya tabbatar da cewa sun cafke wani da ake zargi da garkuwa da kisan wata daliba.

Paul Jeremiah da ake zargi da kisan Damilola ya kasance dan asalin jihar Kaduna ne kuma ya shiga hannun yan sanda ne a ranar Laraba.

Paul ya yanke sassan jikin budurwar

Rahoton Punch ya nuna cewa bayan kashe Damilola, an zargi Paul da cire wasu sassan jikinta masu muhimmanci.

Bayanai da suka fito sun nuna cewa ana zargin Paul Jeremiah da amfani da sassan jikin budurwar ne domin yin tsafi.

Yadda aka kama mai garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

Kisan gilla: An tono gawar matashin da aka birne a daƙi, an kama mutum 1

A karon farko bayan Paul ya kama Damilola ya bukaci a ba shi kudin fansa N400,000 wanda kuma aka ba shi nan take.

Biyo bayan haka ya kara cewa dole sai an ba shi N10m kafin ya sake Damilola wanda a kokarin karɓar kudin ne aka kama shi.

Paul Jeremiah ya nuna wa jami'an tsaro wajen da ya birne Damilola kuma ya ce ya kashe ta ne saboda ta gane fuskarsa.

Filato: An kama mai garkuwa da mutane

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar soji ta yi nasarar cafke ƙasurgumin ɗan bindiga, Husseini Usman da ya addabi mutane da sace sace.

Sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa sun cafke Husseini Usman ne a kauyen Gawunari a karamar hukumar Riyom a jihar Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng