Bayan Ambaliya Ta Kashe Mutum 37, Gwamnati Ta Ba da Umarni kan Madatsar Alau
- Biyo bayan ambaliyar da ta gigita al'umar Maiduguri da ma Arewacin kasar nan, gwamnatin tana shirya kare lamarin a gaba
- Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a gaggauta fara inganta madatsar ruwa ta Alau, wacce fashewarta ya jawo ambaliyar
- Ma'aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli ta bakin Ministanta, Joseph Utsev ta ce kwararru na duba halin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar a - Gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da umarnin fara inganta madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno domin kare afkuwar irin ambaliyar a nan gaba.
Ministan ma'aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Joseph Utsev ne ya bayyana haka a lokacin da ya ja tawaga zuwa Maiduguri.
Jaridar Punch ta tattaro cewa ziyarar ta biyo bayan ambaliya irinta ta farko cikin shekaru 30 da ta shafi mutane sama da miliyan daya a Maiduguri, babban birnin Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da gwamnati ke yi kan ambaliya
Radio Nigeria ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka akwai kwararru da ke duba halin da madatsar Alau ke ciki.
Bayan an gama duba madatsar ne za a dauki matakin gyara ta, sannan a inganta domin kare afkuwar makamancin ambaliyar a gaba.
Ambaliya: Gwamnati ta gargadi yan kwangila
Ministan ma'aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Mista Joseph Utsev ya bayyana cewa ba za a saurara wa duk dan kwangilar da ya yi wasa da aikin madatsar Alau ba.
Ya ce ba za a amince da aiki mara inganci ba ko kuma jinkirta aikin saboda muhimmancin da yake da shi ga rayuwar jama'a.
'Dan majalisa ya ba da gudunmawar ambaliya
A wani labarin kuma dan majalisar wakilai da ke wakiltar yankunan Biu/Bayo/Shani/Kwaya/Kusar, Mukhtar Betara ya yi jajen ambaliya a Borno.
Haka kuma Mukhtar Betara ya bayar da gudummawar Naira Miliyan 100 domin a ci gaba da tallafa wa jama'ar da iftila'in ambaliya ya rutsa da su a Maiduguri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng