Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane a Arewa

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane a Arewa

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar cafke ƙasurgumin ɗan bindiga, Husseini Usman da ya addabi mutane da sace sace a Filato
  • Sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa sun cafke Husseini Usman ne a kauyen Gawunari a karamar hukumar Riyom a jihar Filato
  • Yayin da yake bayani, dan bindigar ya bayyana cewa ya kai munanan hare haren kan al'umma kuma ya yi garkuwa da mutane da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan 'yan ta'adda a jihohi da dama a Arewacin Najeriya.

A jihar Filato, rundunar sojin ta yi nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Husseini Usman.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki bayan fara raɗe raɗin ya rasu

Sojoji
An kama babban dan bindiga a Filato. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa dan ta'addar ya shahara da kai hare hare kan al'umma a jihar Filato.

Sojoji sun kama ɗan bindiga a Filato

A ranar 11 ga Satumba rundunar sojin Najeriya ta cafke ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Husseini Usman a Filato.

An cakfe Husseini Usman ne bayan sojoji sun samu bayanan sirri kan wajen da ya buya kuma suka kai masa samamen ba zata.

Ta'addancin da dan bindigar ya yi

Bayan an cafke shi, dan ta'addar ya bayyana cewa a baya baya ya kai hari ƙauyen Gawunari a karamar hukumar Riyom.

Daily Post ta wallafa cewa harin da dan ta'addar ya kai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu da ba su ji ba-ba su gani ba.

Husseini: 'Dan bindiga ya yi garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani dattijo ɗan shekara 74 yana sata a Masallaci

Haka zalika Husseini Usman ya tabbatar da cewa ya yi garkuwa da mutane a kwanan nan a jihar Filato.

A daya bangaren, sojojin Najeriya sun yi nasarar ƙubutar da wasu mutane da aka yi nufin garkuwa da su a karamar hukumar Kanam.

Matasa sun kubuta a hannun Turji

A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasan garin Moriki a jihar Zamfara sun kubuta daga hannun babban dan ta'adda, Bello Turji bayan ya yi musu barazanar kisa.

Bello Turji ya yi holon matasan a wani bidiyo yana cewa idan ba a kawo masa kudin fansa ba zai kashe su kamar yadda aka yi wa Sarkin Gobir.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng