Ambaliyar Maiduguri: 'Dan Majalisa Ya Ba Gwamnatin Borno Gudunmawar N100m
- Gwamnatin Borno na ci gaba da samun sakon jaje da tallafi daga jagorori da yan siyasa a kasar nan saboda ambaliya
- Mummunan ambaliyar ruwa da jihar ta fuskanta a ranar Talata ta yi sanadin rasuwar mutane fiye da 37 zuwa yanzu
- A wannan jikon, dan majalisa mai wakiltar Biu/Bayo/Shani/Kwaya/Kusar, Mukhtar Betara ya mika tallafin N100m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Dan majalisar Borno mai wakiltar yankunan Biu/Bayo/Shani/Kwaya/Kusar, Mukhtar Betara ya mika jaje ga wadanda iftila'in ambaliya ta fada wa.
Mutane sama da miliyan daya ne su ka fada cikin matsala bayan ambaliya ta mamaye yankunan Maiduguri a ranar Talata.
Jaridar Punch ta wallafa cewa dan majalisar wakilan ya kuma jajanta wa gwamna Babagana Umara Zulum bisa mummunan iftila'in.
N100m: 'Dan majalisa ya tallafa wa Borno
Dan majalisar wakilai, Mukhtar Betara ya bayar da tallafin kudin, Naira Miliyan 100 ga gwamnatin jihar Borno domin taimaka wa wadanda ambaliya ta shafa.
The Cable ta wallafa cewa dan majalisar ya mika gudunmawar ne jim kadan bayan ziyarar duba irin asarar da ambaliyar ta jawo a ranar Alhamis.
Ambaliya: 'Dan majalisa ya mika ta'aziyya
Dan majalisa mai wakiltar Biu/Bayo/Shani/Kwaya/Kusar na jihar Borno a majalisar wakilai ya mika ta'aziyya bayan rasuwar wasu a Maiduguri saboda ambaliya.
Mutum 37 ne aka tabbatar da rasuwarsu zuwa yanzu, yayin da mutane sama da miliyan daya su ka shiga mawuyacin hali sakamakon fashewar madatsar ruwan Alau.
Hon. Mukhtar Betara ya yaba da yadda gwamna Zulum ya gaggauta fara daukar matakan taimakon jama'arsa da ambaliya ta shafa.
Gwamnoni sun yi jajen ambaliyar Borno
A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin jihohin Adamawa da Legas sun ziyarci Borno inda su ka jajanta wa gwamna Babagana Umara Zulum bisa ambaliya.
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya mika tallafin Naira Miliyan 50 da jiragen ruwa ga gwamnatin Borno domin ganin an taimakawa jama'ar jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng