‘Akwai Ƙarancin Abinci:’ Zulum Ya Fadi Halin da Ake ciki Kwanaki 3 da Ambaliya

‘Akwai Ƙarancin Abinci:’ Zulum Ya Fadi Halin da Ake ciki Kwanaki 3 da Ambaliya

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi tsokaci kan halin da al'umma suka shiga bayan ambaliya
  • Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce lallai akwai yunwa kuma sannan ya yi kira kan al'umma su rika taimakon junansu
  • Gwamnan ya ce har yanzu ba su gama tantance adadin mutanen da suka shiga matsala ba saboda ambaliyar ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi magana kwanaki uku bayan ambaliyar ruwa.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce har yanzu suna cigaba da ƙoƙarin kawo dauki ga al'umma kuma suna bukatar agaji.

Borno
Ana yunwa a Borno bayan ambaliya. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Getty Images

Legit ta tattaro abin da gwamnan ya fada ne a cikin wani bidiyo da BBC Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Ana jimamin mutuwar basarake, fitaccen furodusa kuma darakta ya rasu

Ana karancin abinci a Maiduguri

Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce lallai akwai karancin abinci a Maiduguri a halin yanzu kuma hakan ya zo ne saboda ambaliyar ta faru babu shiri ga mutane sun yi yawa.

Farfesa Zulum ya ce daɗin dadawa har yanzu hukuma na kokarin ceto wadanda suka maƙale ne ba wai harkar abinci ta saka a gaba ba.

Gwamnan ya yi kira ga al'ummar jihar da su rika taimakon juna, ya kuma tabbatar da cewa gwamnati na raba N10,000 ga wadanda aka ajiye a sansanoni kullum.

Barnar da ambaliya ta yi a Maiduguri

Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce a hukumance har yanzu ba su fitar da lissafin ƙarshe ba kan barnar da ambaliya ta yi.

Sai dai ya ce a halin yanzu akwai mutane sama da miliyan biyu da suka shiga cikin damuwa da rasa gidajen zama.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya kunyata Janar Abdulsalami ana neman sa hannu a yarjejeniyar zabe

A bangaren lafiya, Gwamna Zulum ya ce an sanar da shi kan tsoron barkewar cututtuka amma suna ƙoƙarin daukan mataki tare da ministan lafiya na kasa.

Maiduguri: Ambaliya ta kashe Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da samun rahotanni kan yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ambaliyar ta kashe yan ta'addar Boko Haram sama da 100 a dajin Sambisa yayin da ruwan ya afka musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng