Yaki Zai Canza: Gwamnan Arewa Ya Sake Zazzafan Shiri kan 'Yan Ta’adda

Yaki Zai Canza: Gwamnan Arewa Ya Sake Zazzafan Shiri kan 'Yan Ta’adda

  • Gwamnatin Katsina ta sake sabon shiri domin fuskantar yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar
  • Dikko Umaru Radda PhD ya amince da ɗaukar yan sa kai da za su rika taimakawa kan dakile yan bindiga a wasu yankuna
  • Haka zalika Dikko Radda ya ware makudan kudi domin sayen kayan aiki da yan sa kai za su rika amfani da su a Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya sake shiri domin fuskantar kalubalen tsaro da ya yi katutu a jihar Katsina.

Gwamnatin jihar Katsina ta shirya tsaf wajen fara ba yan sa kai horo domin daƙile ayyukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

'Akwai ƙarancin abinci:' Zulum ya fadi halin da ake ciki kwanaki 3 da ambaliya

Yan sa kai
Za a horar da yan sa kai karo na biyu a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da jami'in yada labaran gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

Za a dauki yan sa kai su yaki ta'addanci

Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da sake daukar yan sa kai karo na biyu a jihar Katsina domin dakile matsalar tsaro.

Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa yan sa kai na farko da aka dauka sun rage matsalar tsaro a jihar da kashi 30%.

An ware N1.5b domin daukar 'yan sa-kai

Gwamnatin Katsina ta ware zunzurutun kudi N1.5bn domin horar da yan sa kai a jihar karo na biyu.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya kara da cewa za a yi amfani da kudin wajen sayen kayan aiki da za a ba yan sa kai din.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da akidar Boko Haram sun shigo Sakkwato daga kasar waje sun kafa daula

A ina yan sa kai za su yi aiki?

Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa yan sa kai da za a horar za su yi aiki ne a ƙananan hukumomi 10 na jihar domin rage matsalolin yan bindiga.

Ƙananan hukumomin sun hada da Dutsin-ma, Kurfi, Charanci, Danja, Kafur, Bakori da karamar hukumar Funtua.

'Yan sa-kai sun kama harsashi a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa asirin wani mai sayen makami da kayan fada ga yan bindiga masu garkuwa da mutane ya tonu a jihar Katsina.

Yan sa kai a jihar Katsina sun kama tulin harsashi yayin da mugun mutumin ya ɓoye su a cikin wata motar haya da ke tafiya zuwa garin Batsari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng