'Yan Bindiga da Akidar Boko Haram Sun Shigo Sakkwato daga Kasar Waje Sun Kafa Daula

'Yan Bindiga da Akidar Boko Haram Sun Shigo Sakkwato daga Kasar Waje Sun Kafa Daula

  • Mazauna jihar Sakkwato sun shiga fargaba bisa karuwar yan bindiga masu akidar Boko Haram da ake kira Lakurawa
  • Wadannan yan bindiga na shigo wa dazukan Sakkwato ne daga jamhuriyar Nijar da Mali inda su ke kokarin kafa daularsu
  • Yan ta'addan sun yi sansani a dazukan da ke kananan hukumomi uku; Bauni, Tangaza da Gwadabawa a jihar Sakkwato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Al'ummar Sakkwato sun kara fada wa cikin zullumi biyo bayan yadda yan ta'adda daga kasashen ketare ke yin tururuwa zuwa jihar.

An gano wasu yan bindiga masu ra'ayi irin na kungiyar Boko Haram daga kasashen ketare na karuwa a dazukan jihar da ke iyaka da kasashen waje.

Kara karanta wannan

Yaki zai canza: Gwamnan Arewa ya sake zazzafan shiri kan 'yan ta'adda

Sokoto
An samu karuwar yan bindiga a Sakkwato Hoto: Halliru Shehu Tambuwal
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa yan bindigar da aka fi sani da Lakurawa sun kai kusan shekaru uku su na shiga sassan Sakkwato a hankali.

An samu karuwar yan bindiga a Sakkwato

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa yan bindigar Lakurawa sun fara mamaye wasu dazuka da ke da iyaka da kasashen Nijar da Mali.

Garuruwan da su ka fada cikin mawuyacin hali saboda lamarin sun hada da Tsauna da Tunbulukun a karamar Illela.

Sai Bauni, Karma, Munwadata, da Gwaro a karamar hukumar Tangaza da kuma mazauna garin Gudungudun a karamar hukumar Gwadabawa.

Yan bindiga a Sakkwato na mulkin jama'a

Wani mazaunin daya daga cikin yankunan da yan bindigar ke gudanar da ayyukansu ya bayyana cewa ana tilasta masu amfani da dokokin shari'ar musulunci wanda ya saba dokokin Allah.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya a Borno da Bauchi, an shiga fargaba a garuruwan Yobe

Majiyar ta ce yanzu haka Lakurawa na hukunta wadanda ke aske gemu ko sauraron waka, duk da dai su na ba su kariya daga masu garkuwa da mutane.

Yan bindiga sun gargadi jagorin Najeriya

A baya kun ji fitinannen dan ta'adda, Bello Turji ya tura sakon gargadi ga fitaccen lauya, Bulama Bukarti da malamin addinin musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada.

Turji ya yi fatali da shaidar da lauya Bulama Bukarti ya fitar kan harajin da su ka dora wa garin Moriki tare da gargadin ya rika kokarin tabbatar da sahihancin labari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.