Bayan Mutuwar Mutane: Gwamnati ta Fadi Abin da Ya Jawo Ambaliya a Maiduguri

Bayan Mutuwar Mutane: Gwamnati ta Fadi Abin da Ya Jawo Ambaliya a Maiduguri

  • Hukumar raya Arewa maso Gabas ta bayyana cewa rashin karkon gini da kuma cushewar ruwa ya jawo ballewar madatsar ruwa ta Alau
  • An rahoto cewa bayan ballewar madatsar Alau, ambaliya ta afku a Maiduguri, babban birnin Borno wadda ba a taba gani ba a shekaru 30
  • Babban daraktan gudanarwa da harkar kudi na hukumar NEDC, Garba Iliya ya ce a halin yanzu an ba da kwangilar gyara madatsar ruwan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas ta yi magana kan ballewar madatsar ruwa ta Alau lamarin da jawo ambaliya ta mamaye garin Maiduguri, jihar Borno.

Hukumar NEDC ta bayyana cewa rashin kargon gini da kuma cunkushewar ruwa ne ya jawo madatsar Alau ta balle tare da haddasa ambaliya.

Kara karanta wannan

Madatsar Alau: Yadda ambaliya ta mamaye Maiduguri duk da gwamnati ta kashe N171m

Hukumar NEDC ta yi magana kan abin da ya jawo ambaliyar ruwa a Maiduguri
Hukumar NEDC ta alakanta ambaliyar Maiduguri da rashin karkon ginin madatsar Alau. Hoto: Douglas Sacha
Asali: Getty Images

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa ruwan da ya kwararo daga madatsar Alau ya mamaye dubunnan gidaje a Maiduguri, ambaliya mafi muni a shekaru 30.

Dalilin ambaliyar ruwa a Maiduguri

A halin yanzu an rahoto cewa an rufe ofishin aika sako (NIPOST), Gidan Madara da kuma kasuwar Litinin ta Maiduguri (MMM) a sakamakon ambaliyar.

Da yake bayyana musabbabin rushewar madatsar ruwan a ranar Alhamis a Maiduguri, babban daraktan gudanarwa da harkar kudi na hukumar, Garba Iliya, ya ce:

“Manyan katangun madatsar ruwan uku sun gaza rike ruwan da ke ciki, wannan ya jawo ambaliyar da ta mamaye Maiduguri a ranar Litinin."

Ya koka da cewa katangu da sauran muhimman gine-ginen madatsar ruwan sun yi tsufan da suka gaza dauka da kuma rike ruwan da ya jawo ambaliyar.

Ambaliya: Matakin da gwamnati ta dauka

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mutane kusan 50 sun rasu, gidaje 6000 sun lalace a garuruwa 200 a Kano

Ya bayyana cewa, katangun madatsar ruwa ne ke tare ruwa daga ballewa wanda hakan ke kare afkuwar ambaliya tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kasar.

Duk da cewa ba abin da ya samu kofar madatsar ruwan, Garba Iliya ya ce an bayar da kwangilar sake gina katangu da sauran muhimman gine-ginen madatsar ta Alau.

Ya kuma yi gargadin cewa dole ne a kwashe duk wasu tarkace daga kasan madatsar ruwan kafin a fara canza katangun, gami da karfafa babbar kofar madatsar.

Yayin gudanar da aikin madatsar, shugaban hukumar NEDC, Mohammed Alkali ya bada tabbacin cewa zai hada kai da gwamnatin tarayya wajen samar da hanyoyin sa ido.

Mutane 30 sun mutu a Maiduguri

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta ce kimanin mutane 30 ne suka mutu a ambaliyar da ta afku a Maiduguri.

Sai dai kuma mazauna Maiduguri sun ce da yiwuwar adadin ya haura haka domin har yanzun akwai waɗanda ba a gani ba ciki har da ƙananan yara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.