Madatsar Alau: Yadda Ambaliya Ta Mamaye Maiduguri duk da Gwamnati Ta Kashe N171m
- Wani rahoto ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta kashe Naira miliyan 171 domin gyaran madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno
- Rahoton ya nuna cewa gwamnatin ta ware Naira miliyan 171 tsakanin watan Yuni 2023 zuwa Yulin 2024 domin gyara madatsar ruwan
- Sai dai duk da wadannan miliyoyin kudi da aka ware, hakan bai hana madatsar ballewa ba, lamarin da ya jawo ambaliya a Maiduguri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - A makon nan, Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke Arewa maso Gabas ya gamu da iftila'in ambaliyar ruwa sakamakon ballewar madatsar ruwa ta Alau.
Abin da mutane da yawa ke tambaya a kai shi ne: Gwamnati ba ta dauki mataki na dakile madatsar ruwan Alau daga ballewa a wannan shekarar ba?
Gwamnati ta yi aikin gyaran Alau
Bayanai daga shafin Govspend na gwamnatin Najeriya karkashin Shugaba Bola Tinubu sun nuna cewa an ba da aikin gyaran madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan sun nuna gwamnatin Najeriya ta fitar da Naira miliyan 171 domin gyaran madatsar ruwan ta Alau a lokuta daban daban.
Gwamnatin Najeriya ta ware har Naira miliyan 26 a watan Yulin 2024, domin aikin gyara madatsar ruwan.
Rahoton shafin ya nuna cewa gwamnatin ta biya Naira miliyan 171 tsakanin watan Yuni 2023 zuwa Yulin wannan shekarar ta 2024.
Kudin da gwamnati ta kashe kan madatsar Alau
A ranar 4 ga watan Yuni ne aka biya Naira miliyan 23.4 domin gyara madatsar ruwan, inji rahoton SaharaReporters.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa a ranar 20 ga watan Satumba, an kashe kudi naira miliyan 122.4 domin gyaran madatsar ruwa ta Alau.
An rahoto cewa an bayar da kwangilar gyaran madatsar ruwan ne ga kamfanin Hammal and Partners Limited.
An kuma kashe wata Naira miliyan 26 domin aikin gyaran madatsar a ranar 29 ga watan Yulin 2024, kusan wata daya kafin ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri.
Tinubu ya jajantawa 'yan Maiduguri
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna matukar kaduwarsa kan yadda ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a Maiduguri, jihar Borno.
Shugaba Tinubu ya tabbatarwa Gwamna Babagana Umara Zulum cewa gwamnatin tarayya na a shirye domin taimakawa Borno a wannan mawuyacin hali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng