"Mun Damu da Halin da a Ke Ciki": Shugabannin APC Sun Shirya Ganawa da Tinubu

"Mun Damu da Halin da a Ke Ciki": Shugabannin APC Sun Shirya Ganawa da Tinubu

  • Shugabannin jam'iyyar APC a jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja za su gana da gwamnatin Mai girma Bola Tinubu
  • Sakataren kungiyar shugabannin APC na jihohin, Alphonsus Ogar Eba ya bayyana cewa za su tattauna a kan halin da kasar ke ciki
  • Shugabannin sun nuna cewa mutane na korafi a kan tsadar rayuwa da ake fuskanta, amma sun ce za su yi magana da gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugabannin jam'iyyar APC a jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja sun yi magana kan matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.

Shugabannin sun yanke shawarar ganawa da kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan halin da ake ciki a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin duniya sun taso Tinubu a gaba, za a gudanar da zanga zanga a kasashe

Shugabannin APC na jihohi sun yi magana kan halin da ake ciki a Najeriya
Shugabannin APC za su gana da Tinubu kan tsadar rayuwa a Najeriya. Hoto: @DrSRJ
Asali: Twitter

Shugabannnin APC za su gana da Tinubu

Sakataren kungiyar shugabannin APC na jihohi kuma shugaban jam'iyyar na Kuros Riba, Alphonsus Ogar Eba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce ana fama da tabarbarewar rashin tsaro, yunwa, fatara, hauhawar farashin man fetur, kudin wutar lantarki, da sauran kalubale a Najeriya.

Barista Ogar ya sanar da cewa taron shugabannin jam'iyyar da gwamnatin tarayya zai shafi batutuwa da dama musamman dai tsadar rayuwa da 'yan Najeriya ke fuskanta.

Tsadar rayuwa: APC ta magantu a Najeriya

Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai kan wahalhalun da 'yan kasar ke fuskanta a halin yanzu, Barista Ogar ya ce:

"Game da tsadar rayuwa, eh, kowa yana da kuka. Ba za mu nuna cewa ba mu damu da hakan ba kuma mun ce za mu yi ganawar sirri da kwamitin NWC da kuma gwamnati."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu: Shugabannin tsaro 15 na Najeriya da jihohin da suka fito

Barista Ogar ya kuma ce shugabannin jihohin suna aiki tare da kwamitin NWC domin magance rikice-rikicen da ke faruwa a jam’iyyar a wasu jihohi.

APC ta kwancewa Tinubu zani

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC ta amince cewa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun kara jawo tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan.

Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Barista Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ya na mai zargin tsohuwar gwamnati da gaza cika alkawurra.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.