‘Sun Kai Ni Ƙara Wajen Tinubu’ Dangote Ya Fadi Ƙalubalen da Ya ke Fuskanta

‘Sun Kai Ni Ƙara Wajen Tinubu’ Dangote Ya Fadi Ƙalubalen da Ya ke Fuskanta

  • Rukunin kamfanonin Dangote ya koka kan yadda wasu yan kasuwa a Najeriya ba sa sayen kayan da yake fitarwa a matatarsa
  • Mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Devakumar Edwin ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da ya yi
  • Devakumar Edwin ya ce wasu daga cikin yan kasuwa a Najeriya sun kai karar kamfanin Dangote wajen Tinubu a kan farashin man diesel

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rukunin kamfanonin Dangote ya yi magana kan yadda wasu suka koka a kan farashin man diesel dinsa.

An ruwaito cewa wasu yan kasuwa ne suka koka kan yadda farashin ya yi sauki a kasuwannin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana wayyo Allah, 'yan kasuwa sun kara tunkarar Tinubu domin cire tallafin fetur

Dangote
An kai karar Dangote wajen Tinubu. Hoto: Dangote Industries.
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an shigar da korafi kan lamarin har gaban shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kai karar Dangote wajen Tinubu

Rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana cewa wasu yan kasuwa a harkar man fetur sun kai ƙararsa wajen shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An ruwaito cewa an kai matatar Dangote kara wajen Bola Tinubu ne bisa yadda ya karya farashin man diesel a kasuwannin Najeriya.

Dalilin kai Dangote kara wajen Tinubu

Matatar Dangote ta bayyana cewa yan kasuwar da suka kai ƙara sun koka kan cewa farashin man diesel din Dangote yana barazana ga kasuwancinsu.

Business Day ta wallafa cewa mafi yawan yan kasuwar sun kauracewa sayen kaya a wajen Dangote wanda hakan yasa ya ke kai diesel kasashen ketare.

Saboda haka matatar Dangote ta ce maganar tsayar da farashi na cikin kalubalen da ta ke fuskanta a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun gama karaya da matatar Dangote, sun fadi sharadin sayen fetur

Nawa ne farashin diesel din Dangote?

Kafin fara tace man diesel a matatar Dangote ana sayar da man diesel a Najeriya ne a kan N1,100 zuwa N1,000.

Amma a lokacin da matatar Dangote ta fara fitar da diesel farashin ya karye zuwa N9,000 a kasuwannin Najeriya.

An bukaci cire tallafin mai gaba daya

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar yan kasuwar man fetur sun kara fuskantar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan wasu bukatu na musamman.

Cikin abubuwan da yan kasuwar suka bukata wajen Bola Tinubu akwai neman gwamnatin tarayya ta cire hannu a kan tallafin man fetur gaba daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng