Kisan Gilla: An Tono Gawar Matashin da aka Birne a Daƙi, an Kama Mutum 1

Kisan Gilla: An Tono Gawar Matashin da aka Birne a Daƙi, an Kama Mutum 1

  • Rundunar yan sanda a jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 30 da ake zargi da kashe wani matashi dan shekaru 17
  • Yan sanda sun bayyana cewa sun tono gawar matashin mai suna, Adeolu Olubade a cikin wani daki da aka birne shi bayan kashe shi
  • Kakakin yan sandan Legas ya bayyana cewa sun tafi da gawar Adeolu Olubade zuwa asibiti domin bincike da tabbatar da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Rundunar yan sandan jihar Legas ta fitar da sanarwa kan wani mutum da ta kama bisa zargin kisan gilla.

Ana zargin mutumin ne da kashe wani matashi mai shekaru 17 mai suna Adeolu Olubade a yankin Ejigbo.

Kara karanta wannan

Budurwa ta yiwa matashi yankan rago da kwalba, ya mutu har lahira

Legas
An kashe matashi a Legas. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kakakin yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin.

An kashe matashi a Legas

Rundunar yan sanda a jihar Legas ta tabbatar da cewa ta samu rahoto ranar 3 ga Satumba kan an kashe wani matashi mai suna Adeolu Olubade.

Bayan bincike yan sandan sun tabbatar da cewa ana kyautata zaton cewa an kashe matashin ne a ranar 2 ga Satumba tsakanin karfe 4:00 zuwa 7:00 na yamma.

Yadda aka birne matashin cikin daki

Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa bayan sun tsananta bincike sun gano cewa an birne Adeolu Olubade a cikin wani daki bayan an yi masa kisan gilla.

Haka zalika Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa sun tono gawar matashin kuma sun tafi da ita asibiti domin bincike.

Kara karanta wannan

Kano: Matashi ya yi garkuwa da kaninsa 'dan shekara 4, ya nemi fansar Naira miliyan 10

An kama mutum 1 kan kashe matashi

Rundunar yan sanda ta ce ta cafke wani mutum mai shekaru 30 da ake zargi da laifin kisa da birne Adeolu Olubade.

Haka zalika an samu shebur guda daya da ake tunanin da shi aka yi amfani wajen birne Adeolu Olubade a cikin dakin.

Akwa Ibom: An tono gawar yan banga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Akwa Ibom ta tono gawar wasu yan banga da miyagu suka yi wa kisan gilla suka birne su a wani kabari.

Kakakin yan sanda a jihar Akwa Ibom, ASP Timfon John ya tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi da wani basarake.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng