Jami'an DSS da Ƴan Sanda Sun Mamaye Fadar Sarki bayan Fara Raɗe Raɗin Ya Rasu

Jami'an DSS da Ƴan Sanda Sun Mamaye Fadar Sarki bayan Fara Raɗe Raɗin Ya Rasu

  • An fara raɗe-raɗin cewa Sarkin Obokun na Ijeshaland, Oba Adekunle Aromolaran, ya riga mu gidan gaskiya a jihar Osun
  • Jim kaɗan bayan labarin ya fara yaɗuwa, jami'an DSS da ƴan sanda suka garzaya suka mamaye fadar 'marigayi' sarkin
  • Har yanzu masarautar ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba amma wata majiya mai tushe ta tabbatar tda hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Rahotanni sun bayyana cewa an tsaurara matakan tsaro a fadar Owa Obokun na Ijeshaland, Oba Adekunle Aromolaran yayin da aka fara rade-raɗin sarkin ya rasu.

Bayanai sun nuna cewa Sarkin ɗan kimanin shekaru 87 a duniya ya shafe sama da shekara 42 a kan karagar sarauta.

Kara karanta wannan

Babban sarki a jiha ya rasu bayan shafe shekaru 42 a kan karaga

Taswirar jihar Osun.
An fara raɗe-raɗin Sarkin Ijesha a jihar Osun ya riga mu gidan gaskiya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kwantar da basaraken, Oba Aromolaran a asibitin koyarwa na jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa Sarkin na kwance a asibitin yana jiya har zuwa jiya Laraba, 11 ga watan Satumba, 2024.

Majiya ta tabbatar da rasuwar Sarkin Ijesha

Majiya mai tushe a fadar ta tabbatar wa jaridar cewa basaraken ya rasu ne a ranar Laraba da ta gabata.

Wata majiya daga gidan sarautar ta ce:

"Yanzu haka muna nan muna zubar da hawaye da jimami, ba mu ɗaga kiran waya daga waje, kai ma dan dai ba zan iya ganin kiranka na ƙi ɗauka ba ne shiyasa na ɗaga.
"Yanzu haka da nake magana da kai har sun fara kwashe kayan marigayi sarkin daga cikin fada, suna mayar da su wani wurin daban."

Kara karanta wannan

"Ya nuna jarumtaka": Atiku ya kadu da mutuwar babban sarki a kudancin Najeriya

DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki

Bugu da ƙari, wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da cewa tuni dakarun DSS da ƴan sanda suka ƙwace iko da fadar sarkin.

"Jami’an ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun mamaye fadar, sannan kuma an rufe kofofi."

An nemi gwamnan Osun ya sauke sarki

Ku na da labarin an bukaci gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da ya tuge sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi daga sarautar garin.

Malamin addinin gargajiya, Satguru Maharaj Ji ya bukaci hakan daga gwamnan saboda yadda sarkin ke zubarwa masarauta mutunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262