N70,000: Gwamna Ya yi Alkawarin Karin Albashi, Ya Kafa Sharadi

N70,000: Gwamna Ya yi Alkawarin Karin Albashi, Ya Kafa Sharadi

  • Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take wajen fara biyan ma'aikata albashi N70,000
  • Gwamnatin Neja ta bayyana cewa za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin da da zarar wasu abubuwa sun kammala
  • Umaru Bago ya bayyana haka ne a yayin wani taron da kungiyar ma'aikatan lafiya ta MHWUN ta shirya a birnin Minna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Gwamnatin Naje ta tabbatar da cewa za ta biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata N70,000.

Hakan na zuwa ne bayan wasu gwamnoni a Kudu da Arewacin Najeriya sun nuna na'am kan fara karin albashi.

Umaru Bago
Umaru Bago ya yi magana kan karin albashi. Hoto: @HonBago
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Wani Malamin Addini ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira, gwamna ya ɗauki mataki

Neja za ta biya albashi N70,000

Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba ya ce suna shirye da biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Yakubu Garba ya ce gwamnatin Umaru Bago ba za ta yi wani dar dar ba da zarar shirye shiryen karin albashi sun kammala.

N70,000: Sharadin karin albashi a Neja

Pulse Nigeria ta wallafa cewa mataimakin gwamnan Neja ya ce suna jiran gwamnatin tarayya ta kammala shirin karin albashi ne kafin su fara.

Yakubu Garba ya kuma kara da cewa matukar gwamnatin tarayya ta fara biyan sabon albashi kuma suna da kudi su ma za su fara biya.

Gwamnatin Neja ta biya ma'aikatan lafiya

Yakubu Garba ya bayyana cewa gwamna Umaru Bago ya biya ma'aikatan lafiya bashin da suke bin gwamnati.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin ta shirya fara gyaran asibitoci 100 a fadin jihar Neja domin inganta harkar lafiya.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ambaliyar Maiduguri, ruwa ya katse garuruwa 5 a jihar Kaduna

An yi magana kan karin albashi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatocin jihohi da dama ba su fara biyan mafi karancin albashin N70,000 ba kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta amince da shi.

Wani daga cikin kwamitin sabon albashin a Kano ya bayyana cewa kafin fara biyan albashin dole akwai wasu gyare-gyare da za a yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng