Kungiyoyin Duniya Sun Taso Tinubu a Gaba, Za a Gudanar da Zanga Zanga a Kasashe

Kungiyoyin Duniya Sun Taso Tinubu a Gaba, Za a Gudanar da Zanga Zanga a Kasashe

  • Kungiyoyin kwadago da na yan kasuwa na duniya sun fara damuwa da yadda su ka ce gwamnati na take hakkin dan adam a Najeriya
  • Wasu kungiyoyin 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati na duniya sun zargi shugaba Bola Tinubu da cin mutuncin 'yan kwadago
  • Ana shirin yin zanga-zangar kwana daya a manyan biranen kasashen duniya domin nuna damuwa kan halin da kwadago ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kungiyoyin kwadago na duniya karkashin inuwar International Trade Union Conference da Public Service International sun fusata da gwamnatin Najeriya.

Su na zargin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da take hakkin dan Adam ta hanyar kama shugaban kwadago na kasa (NLC), Joe Ajaero.

Kara karanta wannan

Rikici bai kare ba: Za a kai shugaban kwadago asibiti bayan kamun DSS

Tinubu
Kungiyoyin duniya za su yi zanga zanga kan Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A labarin da ya kebanta da jaridar Vanguard, wasu daga cikin kungiyoyin sun shirya daukar matakin da zai yi amo a manyan biranen duniya.

Yan kwadago sun damu da Najeriya

Kungiyar International Trade Union Conference ta nemi shugaba Bola Tinubu ya kawo karshen cin zarafin shugabannin kwadago a Najeriya.

Kungiyar na ganin kama shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero da binciken ofishin kungiyar a babban birnin tarayya da jami'an DSS su ka yi ya saba ka'ida.

Yaushe yan kwadago za su yi zanga zanga?

Majiyoyi a Birtaniya sun bayyana cewa za a gudanar da zanga-zangar kwana daya kafin karshen watan Satumba, 2024 domin adawa da cin zarafin yan kwadago.

Duk da har yanzu ana shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar, amma ana shirin fitowa a manyan biranen kasashen duniya domin a san halin da kasar nan ke ciki.

Kara karanta wannan

'Yan Kudu da Arewa sun hada kai, sun tunkari Tinubu kan tsadar man fetur

Gwamnati ta yi bayanin kama shugaban kwadago

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta musanta zargin da ake yi mata na take hakkin dan adam sakamakon kama shugaban kungiyar kwadago, Kwamred Joe Ajaero.

A bayanin da ta yi kan kama shugaban, gwamnatin ta ce Kwamred Ajaero ya yi biris da gayyatar da hukumomin tsaro su ka yi masa kan zargin daukar nauyin ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.