'Yan Ta'adda Sun Kai Hari a Jihar Neja, Jami'an Tsaro Sun Tura Su Barzahu

'Yan Ta'adda Sun Kai Hari a Jihar Neja, Jami'an Tsaro Sun Tura Su Barzahu

  • Jami'an tsaron Najeriya sun samu nasara kan miyagun ƴan ta'adda da suka kai hari a ƙauyen Bassa da ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja
  • Majiyoyi sun bayyana cewa jami'an tsaron hallaka ƴan ta'adda mutum 12 bayan sun yi musayar wuta yayin harin
  • Wata mata ta rasa ranta yayin da aka harbi wata ƙaramar yarinya a baki da wasu yara maza guda biyu a hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Jami’an tsaro sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a jihar Neja yayin wani musayar wuya.

Jami'an tsaron sun kashe ƴan ta'adda 12 a bayan sun kai hari a ƙauyen Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Jami'an tsaro sun sheke 'yan ta'adda a Neja
Jami'an sun hallaka 'yan ta'adda a jihar Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda aka fafata da ƴan ta'adda

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake kai harin ta'addanci a jihar Neja

Mazauna garin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa ƴan ta'addan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 4:00 na safiyar ranar Laraba.

Sun bayyana cewa bayan ƴan ta'addan sun shigo ƙauyen, sai suka fara harbe-harbe.

Majiyoyi sun bayyana cewa bayan shigowar ƴan ta'addan, jami'an tsaro sun tunkare su inda aka yi musayar wuta.

"Ƴan ta'adda sun kawo farmaki a ƙauyen Bassa da safe. Lokacin da suka shigo sai suka fara harbe-harbe. Cikin ikon Allah sai jami'an tsaro suka tunkare su inda suka hallaka ƴan ta'adda mutum 12."
"A yayin musayar wutan, an harbi wata mata wacce ta rasu, sannan an harbi wata ƙaramar yarinya a baki da wasu yara biyu a hannunsu."

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun lamarin, ya yi alƙawarin ba da cikakkun bayanai daga baya.

Kara karanta wannan

Karshen Bello Turji ya zo, babban hafsan tsaro ya fadi lokacin cafke jagoran 'yan bindiga

Sai dai, bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Jami'an tsaro sun tono bama-bamai a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun tono wasu abubuwan fashewa da bama-bamai a wurare daban-daban a wasu sassan jihar Neja.

Daga cikin wuraren da aka tono bama-baman har da Galadima-Kogo da ke ƙaramar hukumar Shiroro, Mutun-ɗaya a Mangu da unguwar Gbeganu a Minna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng