Tsadar Man Fetur Ya Tilastawa Gwamna Karawa Ma'aikata Hutu a Kowane Mako

Tsadar Man Fetur Ya Tilastawa Gwamna Karawa Ma'aikata Hutu a Kowane Mako

  • Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya kawo hanyar saukakawa al'ummarsa bayan karin kudin man fetur a Najeriya
  • Gwamnan ya kara kwanakin hutu ga ma'aikatan jihar musamman ga wadanda ke mataki na daya zuwa 14 a aikin gwamnati
  • Sai dai gwamnan ya ce wadanda ke mataki na 14 zuwa 17 za su cigaba da cin gajiyar hutu na kwana daya kamar yadda ya ke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Yayin da ake mawuyacin hali na tsadar mai, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tausayawa jama'a.

Gwamna Dapo Abiodun ya kara hutun kwanaki biyu ga wasu ma'aikata yayin da wasu suka samu karin kwana daya.

Kara karanta wannan

'Akwai ƙarancin abinci:' Zulum ya fadi halin da ake ciki kwanaki 3 da ambaliya

Gwamna ya rage kwanakin zuwa aiki ga ma'aikata
Gwamna Dapo Abiodun ya rage yawan kwanakin aiki ga ma'aikata a jihar Ogun. Hoto: Dapo Abiodun.
Asali: Facebook

Gwamna ya saukakawa al'umma kan tsadar mai

Channels TV ta ce shugaban ma'aikatan jihar, Kehinde Onasanya shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 11 ga watan Satumbar 2024.

Onasanya ya ce Gwamna Abiodun ya himmatu wurin tabbatar da inganta rayuwar ma'aikatan jihar.

Ya ce gwamnan ya dauki wannan mataki ne domin saukakawa al'umma duba da yadda suke cikin wani hali a yanzu, Pulse ta ruwaito.

Yadda aka ba ma'aikata hutu a jihar Ogun

Ma'aikata da ke mataki na daya zawa 14 za su samu karin hutun kwanaki biyu yayin da daga mataki na 14 zuwa 17 za su cigaba da samun karin hutun kwana daya kamar yadda ake ciki.

Gwamnan har ila yau, ya bukaci masu kula da bangaren kudi a ma'aikatu su tabbatar sun dabbaka tsarin da gaggawa.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwar fetur sun harzuka shi, gwamna ya kara barazana, ya rufe gidajen mai

Gwamna ya ba ma'aikatu umarni kan aiki

Ya bukace su da su tabbatar sun tsara komai yadda zai tafi daidai duk da rashin wasu kwanakin a mako.

A watan Yulin 2023, gwamnan ya yi karin kwana daya ga dukkan ma'aikatan jihar domin ragewa al'umma radadin cire tallafin mai.

Ma'aikaci a jihar Gombe ya yi magana da Legit Hausa kan matakin gwamnan Ogun game da farashin mai.

Abubakar Sadik ya ce tabbas gwamnan ya tallafa domin ragewa ma'aikata halin da suke ciki.

Sadik ya ce su ma'aikatan Gombe damuwarsu yanzu ya za a yi a biya su mafi ƙarancin albashi.

Ya roki gwamnan da ya yi gaggawar fara biyan mafi ƙarancin albashi duba da yadda rayuwa da kasance.

Tsadar mai: Gwamnatin Kwara ta saukakawa al'umma

Kun ji cewa ana cikin mawuyacin hali bayan kara farashin mai a Najeriya, Gwamnatin jihar Kwara ta agazawa al'ummarta.

Kara karanta wannan

Mawakin Musulunci ya fadi dalilin yin murabus daga matsayin hadimin gwamna

Gwamnatin ta ba da umarnin samar da bas musamman a cikin birni domin zirga-zirgar jama'a wurare daban-daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.