Wani Malamin Addini Ya Daɓawa Matarsa Wuƙa har Lahira, Gwamna Ya Ɗauki Mataki

Wani Malamin Addini Ya Daɓawa Matarsa Wuƙa har Lahira, Gwamna Ya Ɗauki Mataki

  • Ana zargin wani Fasto, Elijah Emeka Ibeabuchi ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Gwamnatin jihar Anambra ta hannun ma'aikatar mata da walwalar jama'a ta ba da umarnin gudanar da bincike kan kisa matar
  • Dangin mamaciyar sun bayyana cewa da farko mijin ya faɗa masu faɗowa ta yi daga bene amma da suka ga gawar suka gane akwai wata a ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Gwamnatin Anambra karƙashin jagoranci Gwamna Charles Soludo ta ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan kisa wata mata, Misis Ogechukwu Okafor.

Gwamnatin jihar ta ɗauki wannan matakin ne ta hannun ma'aikatar kula da harkokin mata da walwalar al'umma ta jihar da ke Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Taswirar Anambra.
Gwamnatin Anambra ta lashi takobin binciko gaskiya kan kisan wata mata Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Anambra: Ana zargin fasto ya kashe matarsa

Jaridar Punch ta tattaro cewa ana zargin mijin matar mai suna, Mista Elijah shi ne ya yi ajalinta.

Lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Agusta, 2024, amma dangin mamaciyar ne suka kai rahoto ga ma’aikatar bayan ganin abin tuhuma a tattare da mijin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamishinar harkokin mata da walwalar jama’a, Chidimma Ikeanyionwu ya fitar ranar Laraba.

A cewar Ikeanyionwu, wanda ake zargin Fasto ne kuma ya aikata laifin ne a ƙauyen Nimo da ke karamar hukumar Njikoka a Anambra, cewar Tribune Nigeria.

Yadda malamin cocin ya kashe matarsa

Sanarwar ta ce:

"Kawun matar Samuel Onuorah tare da wasu ƴan uwansu ne suka shigar da ƙorafi a ma'aikatar mata, sun ce an kira su a waya ne kawai aka sanar da su cewa ta faɗo daga bene ta mutu.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Rundunar sojoji ta mika ta'azziyya Borno, za a taimaka wa jama'a

"Mista Elijah Emeka Ibeabuchi, wanda ya fito daga Nimo a karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra, shi ne mijin marigayiya Ogechukwu Okafor.
"Kawun matar ya ce daga baya suka gano ɗiyarsu ba faɗowa ta yi daga bene ba kamar yadda mijinta ya faɗa, sun gano shi ne ya caka mata wuƙa a wuya da ƙirji."

Da take martani kan lamarin, kwamishinar mata, Ify Obinabo ta buƙaci masu ruwa da tsaki su marawa gwamnati baya wajen tabbatar da an yi wa mamaciyar adalci.

Mahara sun kashe ɗan sanda a Anambra

A wani rahoton kuma mutum ɗaya ya mutu da ƴan bindiga suka kai mummunan farmaki a hedkwatar ƴan sanda da ke garin Oba a jihar Anambra.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga ya ce maharan sun riƙa jefa bama-baman kwalabe a wannan harin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262