Gwamnatin Kano Ta Bankado Ma'aikatan Lafiya da Ke Tafka Mata Sata, Ta Dauki Mataki

Gwamnatin Kano Ta Bankado Ma'aikatan Lafiya da Ke Tafka Mata Sata, Ta Dauki Mataki

  • Gwamnatin Kano ta gargadi wasu ma'aikatan lafiya da ta kira da “marasa kishi,” da su kauracewa satar magunguna a asibitocin jihar
  • Shugaban hukumar kula da magunguna ta Kano (DMCSA), Gali Sule ya ce sun gano ma'aikatan lafiya na satar magungunan jihar
  • A cewarsa, ma’aikatan marasa kishi na hana marasa lafiya sayen magunguna a farashi mai sauki a cibiyoyi da asibitoci mallakin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bankado yadda wasu ma'aikatan lafiya ke sacewa tare da sayar da magunguna da wasu kayayyakin kiwon lafiya a jihar.

A wannan gabar, ta ce ta dauki matakan dakile karkatar da magunguna da kayayyakin kiwon lafiya daga asibitoci da cibiyoyin lafiya mallakar gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya a Borno da Bauchi, an shiga fargaba a garuruwan Yobe

Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan ma'aikatan lafiya da ta gano suna satar magunguna
Gwamnatin Kano ta gargadi ma'aikatan lafiya da ke sata da sayar da magungunan jihar. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Gali Sule, shugaban hukumar kula da magunguna da kayayyakin kiwon lafiya ta jihar Kano ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai (NAN) a Kano, a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: An gano ma'aikata na sata a asibiti

Shugaban hukumar ta DMCSA ya ce an dauki matakin ne domin fadakar da jama’a kan abubuwan da ke faruwa a cibiyoyin kiwon lafiya na Kano.

Ya ce hukumar na da babban kalubale da wasu cibiyoyinta inda aka gano wasu ma’aikatan lafiya na karkatar da magunguna da sauran kayayyakin kiwon lafiya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ya gargadi masu aikata laifin, wadanda ya kira da “marasa kishin kasa” da su kauracewa dabi'ar ko su fuskanci hukunci idan an kama su.

Gwamnatin Kano ta gargadi 'marasa kishi'

A cewarsa, ma’aikatan 'marasa kishi' na tura marasa lafiya zuwa shagunan sayen magunguna a wajen asibiti maimakon su bari su sayi na asibitin a farashi mai rahusa.

Kara karanta wannan

'Yan takarar NNPP 20 na ta'ammali da kwayoyi a kano? NDLEA ta yi karin haske

“Akwai wasu ma'aikata marasa kishin kasa da ke yin zagon kasa ga yunkurinmu na samar da sauki ga marasa lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya da ke fadin jihar nan.
“Muna da tsarin sa ido mai karfi kuma da zarar an kama mutum zai fuskanci hukunci mai tsanani kamar yadda dokar ma’aikatan jihar ta tanada."

- A cewar shugaban DMCSA.

Za a binciki badakalar magunguna

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnati za ta gudanar da bincike kan zargin badakalar magunguna ta kimanin Naira biliyan daya.

Tsohon dan jarida, Dan Bello ne ya yi ikirarin gwamnatin Kano ta ba dan uwan Rabiu Kwankwaso kwangilar magungunan ba bisa ka'ida ba, zargin da gwamnan ya ce bai da masaniya a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.