Ana Fargabar Dabbobi Sun Fita a Borno, Macizai Sun Harbi Yan Gudun Hijira a Jihar Arewa
- An samu harbin macizai da dama ga wadanda suke zaune a sansanin yan gudun hijira a jihar Benue da ke Arewacin Najeriya
- An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wurare guda uku da aka ajiye yan gudun hijira a karshen watan Agusta da farkon Satumba
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta ce ta dauki matakan gaggawa amma duk da haka akwai buƙatar karin kayan kiwon lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Masu zama a sansanin yan gudun hijira a jihar Benue na fuskantar barazanar harbin macizai.
An ruwaito cewa an samu harbin macizai da suka kusan 20 a wasu wuraren da aka ajiye yan gudun hijira.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta fara daukan mataki kan lamarin.
Macizai sun harbi yan gudun hijira
Rahotanni sun tabbatar da cewa macizai sun harbi yan gudun hijira 16 a wasu sansanoni a jihar Benue a Arewacin Najeriya.
Harbin ya faru ne a sansanonin yan gudun hijira guda uku a makon karshe na watan Agusta da makon farko na watan Satumba.
Yan gudun hijira ba su mutu ba
Daraktan Hukumar NEMA a jihar Benue ne ya tabbatar da samun harbin macizai a sansanonin yan gudun hijira a yau Laraba.
Vanguard ta wallafa cewa shugaban NEMA, James Lorpuu ya ce ba a samu dan gudun hijira ko daya da ya mutu ba sakamakon cizon maciji.
NEMA ta dauki matakin kan harbin macizai
Hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Benue ta bayyana cewa bayan samun cizon macizai ta yi feshin magani a sansanin yan gudun hijira.
Ta ce feshin zai rage yaɗuwar macizan a sansanin kuma har yanzu tana bukatar ƙarin kayan tallafi musamman wadanda suka shafi lafiya.
Yan gudun hijira sun roki Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa yan gudun hijira sun roki Shugaba Bola Tinubu ya tausaya musu wurin dawo da Ministar jin kai, Dakta Betta Edu.
'Yan gudun hijirar da ke sansanoni a jihohin Borno da Niger a Arewacin Najeriya sun yi rokon ne ganin yadda Edu ke tallafa musu lokacin tana ofis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng