Shugaban Majalisa Akpabio Ya Kadu da Ambaliya a Jihohin Arewa, Ya Sha Alwashi

Shugaban Majalisa Akpabio Ya Kadu da Ambaliya a Jihohin Arewa, Ya Sha Alwashi

  • Shugaban majalisar dattawa, Rt. Hon. Godswill Akpabio ya bayyana kaduwa bisa ambaliya da aka yi a jihohin Borno da Bauchi
  • A sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Eseme Eyoboh ya fitar, Akpabio ya mika jajensa ga mazauna jihohin
  • Mutane da dama su ka rasu, yayin da aka rasa dubban muhallai a Borno da Bauchi da ambaliya ta yiwa mummunar barna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawan kasar nan, Sanata Godswill Akpabio ya taya mazauna Borno da Bauchi alhinin ambaliyar ruwa.

A ranar Talata ne mummunar ambaliya ta daidata jama'a a Borno da Bauchi, inda har yanzu ba a kammala tattara adadin wadanda su ka rasu ba

Kara karanta wannan

Wani Malamin Addini ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira, gwamna ya ɗauki mataki

Goodwill
Shugaban majalisa ya yi jajen ambaliya a Arewa Hoton: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

The Guardian ta tattaro cewa a sanarwar da mai magana da yawun Apkabio, Eseme Eyoboh ya fitar, ya ce shugaban na mika jaje ga jama'ar da iftila'in ya rutsa da su.

Ambaliya: Apkabio ya jajanta wa Kashim Shettima

Wani mai amfani da shafin Facebook, Frater Effiom Anso ya wallafa sakon ta'aziyyar shugaban majalisa, Godswill Akpabio ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Haka kuma ya jajanta wa dukkanin yan majalisu da masu rike da sarautun gargajiya da lamarin ya afka wa jama'arsu a Borno da Bauchi.

Akpabio ya fadi shirin majalisa bayan ambaliya

Godwill Akpabio ya tabbatar da cewa majalisar kasar nan a shirye ta ke ta bayar da gudunmawar da za a bukata daga gare ta kan ambaliya.

A jihar Bauchi, mutum 24 ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da gonaki sama da 300 su ka lalace, inda har yanzu ake tattara bayanan barnar ambaliyar a Borno.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya a Borno da Bauchi, an shiga fargaba a garuruwan Yobe

Ana fargabar ambaliya a Yobe

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Yobe ta yi gargadin cewa akwai fargabar ambaliya za ta mamaye kananan hukumomi tara a jihar bayan cikar madatsun ruwa.

Gwamnati ta bukaci jama'a su kwana cikin shirin ko-ta-kwana yayin da aka jibge jami'an hukumar bayar da agaji a yankunan da ake fargabar za a samu ambaliya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.