'Yan Takarar NNPP 20 na Ta'ammali da Kwayoyi a Kano? NDLEA Ta Yi Karin Haske

'Yan Takarar NNPP 20 na Ta'ammali da Kwayoyi a Kano? NDLEA Ta Yi Karin Haske

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar Kano ta gyara labarin samun wasu 'yan takarar NNPP da ta'ammali da kwayoyi
  • A safiyar yau ne aka samu labarin an samu wasu 'yan takara a zaben kananan hukumomin Kano mai zuwa da amfani da miyagun kwayoyi
  • A zantawarsa da Legit, jami'in hulda da jama'a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya ce ba haka labarin ya ke ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen jihar Kano ta ce an jirkita labarin 'yan takarar zaben kananan hukumomi mai zuwa kan amfani da kwaya.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya a Borno da Bauchi, an shiga fargaba a garuruwan Yobe

Hukumar ta tabbatar da cewa an samu wasu yan takara da aka gano su na ta'ammali da miyagun kwayoyi bayan an yi masu gwaji.

NDLEA
NDLEA ta yi bayani kan yan takara masu ta'ammali da kwaya a Kano Hoto: Sadiq Muhammad
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jami'in hulda da jama'a na NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya ce an juya masu labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu yan takara da shan kwaya

Mai magana da yawun hukumar NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya bayyana cewa tabbas an samu yan takara 20 da aka tabbatar da su na amfani da kwayoyi.

Amma a cewarsa babu inda hukumar ta bayyana cewa 'yan NNPP ne, ko masu neman kujerar shugabannin karamar hukuma ko kansiloli.

NDLEA za ta fitar da binciken kwaya

Hukumar NDLEA a Kano ta shawarci jama'a su guji yada labaran da ba a tabbatar da yadda ya ke ba domin gujewa yin karya.

Kara karanta wannan

"Zai yi wahala," NNPP ta yi martani kan samun 'yan kwaya a cikin 'yan takararta

Hukumar da ke gwada 'yan takarar kananan hukumomi a Kano yanzu haka ta ce sannu a hankali za ta fitar da sakamakon bincikenta idan ya kammala.

NNPP ta yi watsi da gwajin NDLEA

A baya kun ji cewa jam'iyyar NNPP a Kano ta musanta cewa yan takararta ne mutum 20 da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta gano su na ta'ammali da kwaya.

Shugaban NNPP a Kano, Dr. Hashim Dungurawa ne ya bayyana haka, amma ya ce ta yiwu na'urorin da NDLEA ta yi amfani da su sun fuskanci matsala, tun da dan Adam ne ya yi su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.