Masu Zanga Zangar da Aka Kama Sun Yi Nasara, Kotu Ta Yanke Hukunci kan Buƙatarsu
- Babbar kotun tarayya ta amince da belin mutum 10 da aka kama a lokacin zanga zangar adawa da yunwa a Najeriya
- A zaman ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, mai shari'a Emeka Nwite ya ba da belin waɗanda ake tuhumar kan N100m
- Kotu ta ce tsarin shari'a a Najeriya yana da dokoki, duk wanda ake tuhuma ba zai taɓa zama mai laifi ba sai an tabbatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba da belin mutum 10 daga cikin masu zanga-zangar yunwa da aka kama a Najeriya.
Idan ba ku manta ba jami'an tsaro sun cafke matasa da ƙananan yara a lokacin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da aka yi tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Kotu ta amince da belin masu zanga-zanga
Punch ta tattaro cewa bayan gurfanar da su kan tuhumar cin amanar ƙasa, kotun mai zama a Abuja ta bada belin masu zanga-zanga 10 kan N100m, kowane N10m.
Mai shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya ne ya yanke wannan hukunci a zaman shari'ar ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, 2024.
Da yake karanto hukuncin, alkalin kotun ya ce tsarin shari’ar manyan laifuka na Najeriya yana da sharudda ga mai gabatar da kara da wanda ake kara.
Nwite ya amince da bayanin lauyan waɗanda ake ƙara na 1, 2, 3 da na 4 cewa duk wanda ake tuhuma ba mai laifi ba ne har sai an tabbatar da laifinsa.
Meyasa kotu ta bada belin masu zanga-zangar?
Bisa wannan hujja ne, alkalin ya ba da belin dukkan mutane 10 da ake tuhuma da laifin cin amanar ƙasa a lokacin zanga-zangar da aka yi.
A rahoton Daily Trust, alkalin ya ce:
"Na duba bayanan kowane ɓangare kuma na amince da bayar da belin waɗanda ake tuhuma duk da zargin da ake yi masu.
“Saboda haka na ba da belim kowane ɗaya da ake ƙara kan N10m da wanda zai tsaya masa."
Zanga-zanga: Gwamna ya cikawa matasa alƙawari
A wani rahoton kuma gwamnan Akwa Ibom ya cika alƙawarin da ya ɗauka na kyautatawa matasan jihar idan suka ƙi shiga zanga-zanga.
Mai girma Gwamna Umo Eno ya ba da kyautar N310m domin rabawa ga matasa a ƙananan hukumomi 31 na jihar Akwa Ibom.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng