Hajj 2025: Gwamna Ya Tsayar da Ranar Fara Karbar Kafin Alkalamin N6.5m
- Gwamnatin Bauchi ta tsayar da kudin kafin alkalami da za a karba daga hannun maniyyata aikin hajjin 2025
- Gwamna Bala Mohammed ya amince a fara karbar Naira Miliyan 6.5 daga hannun maniyyatan a matsayin ajiya
- Za a fara karbar kafin alkalamin ne a ranar Laraba, 11 Satumba, 2024 kafin a kayyade kudin aikin hajji a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya umarci hukumar aikin hajjin jihar da ta fara karbar kafin alkalami daga maniyyatan aikin hajjin 2025.
Gwamnan ya amince a fara karbar Naira Miliyan 6.5 daga ranar Laraba, 11 Satumba, 2024 a kafin a tsayar da ainihin kudin aikin hajjin badi.
Jaridar Punch ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na hukumar aikin hajjin Bauchi, Muhammad Yunusa ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar.
Nawa ne kafin alkalamin aikin hajjin 2025?
Hajj reporters ta wallafa cewa hukumar aikin hajjin Bauchi ta shawarci maniyyatan aikin hajjin 2025 su fara ajiye Naira Miliyan 6.5.
Wancan adadi shi ne mafi karanci da za su iya ajiye wa, amma za su iya biyan har Naira Miliyan takwas domin ba su damar fara shirin aikin hajji da wuri.
Hajj 2025: Dalilin tsuga kudin zuwa Saudi
Hukumar aikin hajjin Bauchi ta bayyana cewa an sanya mafi karancin kafin alkalamin aikin hajjin badi ne duba da yadda aka biya a shekarar 2024.
Kakakin hukumar, Muhammad Yunusa ya ce a aikin hajjin da ya gabata, musulmi sun biya har Naira Miliyan 8, kuma an samu raguwar darajar Naira.
An sasanta rikici saboda aikin hajji
A wani labarin kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Oyo ta dauki matakin kawo sulhu bayan rikici ya barke tsakanin basaraken Ogbomosho da limamin jihar kan aikin hajji.
Basaraken da ke sarautar Ogbomoso, Oba Ghandi Afolabi Olaoye ya fusata kan yadda limami Yunus Tella Olushina Ayilara ya yi gaban kansa wajen tafiya aikin hajji ba tare da izini ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng