'Yan Sanda 39 a Kauyuka 200," Gwamna Radda Ya Fayyace Matsalar Tsaron Katsina

'Yan Sanda 39 a Kauyuka 200," Gwamna Radda Ya Fayyace Matsalar Tsaron Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya bayyana adadin yan sandan da ke kula da karamar hukuma a jiharsa duk da rashin tsaro
  • Gwamna Radda ya ce yan sanda 39 ne ke kula da kauyuka akalla 200 a kowacce karamar hukuma, kuma babu isassun makamai
  • Ya ce duk da miyagun yan ta'addan da ake da su a jihar, babu yadda za a yi yan sanda su iya tsare rayuka da dukiyoyin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Gwamna Umaru Dikko Radda ya bayyana cewa jiharsa ta Katsina ba ta da isassun jami'an tsaro ko makaman da za a yaki ta'addanci.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya koka da sace mutane a asibitin Kaduna, ya fadi abin da ake bukata

Gwamna Radda ya ce a yanzu haka, akwai kauyuka akalla 200 a mazabu 10 a cikin karamar hukuma daya, kuma jami'a tsaron da ke kula da su ba su da yawa.

Dikko Radda
Gwamnan Katsina ya koka kan rashin jami'an tsaro Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

A hirar da gwamna Dikko Radda ya yi da tashar DW, ya bayyana cewa duk yawan kauyukan da ake da su a karamar hukuma, yan sanda 39 kawai ke kula da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda ba su da makamai," Gwamna Radda

Gwamnatin Katsina ta ce ta bayyana cewa a cikin yan sanda 39, bindigu tara kawai ake da su, kuma ba dukkanninsu ne ke aiki ba.

Jaridar The Cable ta wallafa cewa gwamnan jihar, Umaru Dikko Radda ne ya bayyana haka, inda ya ce bindigu biyar ne kadai ke aiki a cikin tara.

Katsina: Yan sanda sun yi kadan inji gwamna

Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya bayyana cewa jami'an tsaro da makaman da ake da su ba za su wadata a yaki ta'addanci ba.

Kara karanta wannan

Gwamna zai fara ba mutane bindiga domin gwabzawa da yan ta'addan Arewa

Gwamnan ya kara da cewa babu hanyar da makamai biyar za su kare kauyuka 200 yayin da yan ta'adda rike da mugayen makamai su ka kai farmaki.

Gwamna zai ba jama'a bindigu

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Katsina ta bayyana cewa a shirye ta ke ta raba makamai ga mutanen da ke son yaki da ta'addanci a yankunansu.

Gwamna Dikko Yadda ya ce duk jama'ar da su ka shirya kare kansu daga harin yan ta'adda su hada kawunansu wuri guda, su kuma sanar da gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.