Mulkin Tinubu: Malami Ya Hango Shekarar da Tsadar Rayuwa Za Ta Kare a Najeriya

Mulkin Tinubu: Malami Ya Hango Shekarar da Tsadar Rayuwa Za Ta Kare a Najeriya

  • Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen matsalolin tattalin arziki za su mamaye wa'adin farko na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Fasto Ayodele ya bayyana shakkunsa kan cewa Shugaba Tinubu na da mafita ga yawan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yau
  • Fitaccen malamin ya kuma bayyana abin da ya gani na game da lokacin da 'yan Najeriya za su samu sauki daga wahalhalun rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Primate Elijah Ayodele, ya zana mummunan hoto kan abin da zai je ya dawo dangane manufofin gwamnatin tarayya da ta tsara na gajere da matsakaicin lokaci kan tattalin arziki.

Wannan na zuwa ne bayan dagewar da gwamnatin Bola Tinubu ta yi na ganin ta dawo da martabar kasar nan ba da dadewa ba tana mai kira ga ‘yan kasar da su jure.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki Musulmi ya zabgawa malamin addini mari a bidiyo, ya fadi dalili

Fitaccen malamin addini ya gano lokacin da za a samu saukin tsadar rayuwa a Najeriya.
Primate Ayodele ya yi sabon hasashe game da tsadar rayuwa a Najeriya. Hoto: @officialABAT, @primate_ayodele
Asali: Twitter

Malami ya yi hasashen tsadar rayuwa

A wani bidiyo da ya wallafa a shafin X, fitaccen malamin ya hasasho cewa za a iya daukar har zuwa 2027 kafin a fara farfadowa daga mawuyacin halin da ake ciki.

A yanzu da farashin fetur ya ke tsakanin N900 zuwa N1,200, Primate Ayodele ya yi hasashen cewa tattalin arziki zai kara tabarbarewa wanda zai haifar da wahalhalu ga 'yan kasar.

Fitaccen malamin ya nuna cewa akwai sauran kalubale da ke fuskantar Najeriya kasancewar shugaban kasarta ba zai iya biyan bukatun 'yan kasar ba.

"Tinubu ba zai iya ba" - Ayodele

A cikin faifan bidiyon, an ji malamin na cewa:

"Ya zuwa yanzu, zan iya fada maku cewa har yanzu akwai sauran rudani. Akwai sauran kalubale a gaban Najeriya domin Tinubu ba zai iya biyan bukatun 'yan kasar ba.

Kara karanta wannan

"Na yi wasiyya idan an sace ni," Sheikh Bello Yabo ya sha alwashin cafko yan bindiga

"A cikin wadannan shekaru da suka rage, Najeriya ba za ta samu wani ci gaba ba."

"Abin da zai faru a 2027" - Ayodele

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen malamin addinin Kirista, Primate Babatunde Ayodele ya yi hasashen cewa za a samu "tashin hankula" a lokacin babban zaben 2027.

Primate Ayodele ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tashi tsaye kuma ya yi abin da ya dace gabanin babban zaɓe na gaba domin kare faruwar tashin tashinar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.