Bayan Iftila'in Maiduguri: Gwamnati Ta Dauki Sabon Matakin Magance Ambaliyar Ruwa
- Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya wasu sababbin tsare tsare da su taimaka wajen magance matsalolin ambaliyar ruwa a fadin kasar nan
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci Maiduguri da ambaliya ta yiwa mummunar barna
- Shettima ya ce gwamnati na kokarin kwashewa tare da canjawa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa matsugunni kafin lamarin ya lafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta shirya wani sabon tsari na tunkarar kalubalen ambaliyar ruwa a Najeriya.
Kashim Shettima ya bayyana cewa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kammala tsara hanyoyin magance ambaliyar ruwa duk da cewa dalilan faruwar iftila'in na da yawa.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar Talata, 10 ga Satumba kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya yi magana a Borno
An rahoto cewa Kashim Shettima ya je Maiduguri ne domin yin nazari game da mummunar ambaliyar ruwa da ta raba al’ummar garin da muhallansu.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta ba da fifiko ga jin dadin mutanen da iftila'in ambaliyar ruwan ya shafa.
Mataimakin shugaban kasar ya ce:
“Na kadu matuka da ambaliyar ruwa da ta mamaye Maiduguri da kewaye. Ina jajantawa iyalan da suka rasa matsugunansu da hanyar dogaro da rayuwarsu sakamakon ambaliyar.
“Ana ci gaba da kokarin kwashewa da kuma nemawa mazauna yankunan da abin ya shafa wani matsugunnin, tare da tabbatar da samar da abinci, da magunguna har sai lamarin ya daidaita.
Gwamnati ta dauki mataki kan ambaliya
Gidan talabijin NTA ya rahoto Kaashim Shettima ya ci gaba da cewa:
"A matsayin martani ga yanayin ambaliyar ruwa na 2024, mun aiwatar da cikakkun tsare-tsare na gaggawa tare da daukar matakan da suka dace don rage tasirin iftila'in.
"Duk da wadannan shirye-shirye, tsananin wannan ambaliya ya zarce hasashen da muka yi, wanda ambaliyar Maiduguri ce mafi muni cikin sama da shekaru talatin.
Kamar sauran jihohin da ke fuskantar irin wannan ambaliya, za mu dora da tsare-tsaren da aka fara a baya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno."
Tinubu ya tura Shettima Borno
Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya je Maiduguri, jihar Borno domin ganin barnar da ambaliyar ruwa ta yi.
Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a Abuja yana mai nuna kaduwarsa kan yadda ambaliyar ta mamaye birnin Maiduguri bayan madatsar ruwa ta Alau ta balle.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng