'Yan Kasuwa Sun Gama Karaya da Matatar Dangote, Sun Fadi Sharadin Sayen Fetur
- Yan kasuwar man fetur sun bayyana damuwa kan yadda matatar Dangote ta ki cewa komai kan farashin da za ta sayar masu
- Kungiyar dillalan mai ta IPMAN ta ce ba za ta sayi fetur daga matatar Dangote ba matukar farashin ya haura yadda su ke saye a yanzu
- Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Maigandiya bayyana cewa a yanzu haka su na sayen man fetur a kan N1, 200 kowace lita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Dillalan man fetur a kasar nan sun bayyana damuwa kan yadda har yanzu matatar Dangote ba ta ce komai kan farashin fetur ba.
Tun a baya dai hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote ya bayyana cewa su na jiran kamfanin mai na kasa (NNPCL) da Bola Tinubu kan farashinsu.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa a kalaman shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi har yanzu ba su ji komai game da farashin feturin Dangote ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Za mu iya shigo da fetur" - IPMAN
Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta ce yan kasuwa za su iya ci gaba da shigo da fetur daga wajen kasar nan.
Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Abubakar Maigandi ya ce yanzu haka su na sayen fetur a kan N1,200 kowace lita.
Shugaban ya kara da cewa matukar farashin feturin Dangote ya haura haka, ba za su saya daga wajensa ba.
IPMAN na tattaunawa da 'yan kasuwa
Kungiyar IPMAN ta bayyana cewa har yanzu ba ta san farashin da matatar Dangote za ta sayar masu da fetur ba.
Kungiyar ta ce saboda haka ne ma ta ke tattaunawa da abokan huldarta da ke kasashen waje kan ci gaba da shigo da fetur Najeriya.
IPMAN ta magantu kan farashin fetur
A baya mun ruwaito cewa kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta bayyana cewa za a iya samun matsala da sayen fetur daga matatar Dangote da ta fara tace mai a Legas.
Kungiyar ta bayyana cewa ba lallai ta iya sayen fetur daga matatar ba saboda zai yi masu tsada, a dai-dai lokacin da ake takun saka tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Dangote.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng