Yan Bindiga Sun Sace Bello Yabo? Shehi Ya Yi Maganar 'Garkuwa' da Shi da 'Kamen' DSS

Yan Bindiga Sun Sace Bello Yabo? Shehi Ya Yi Maganar 'Garkuwa' da Shi da 'Kamen' DSS

  • Babban malamin Musulunci, Sheikh Bello Yabo ya yi magana kan rade-radin cewa yan bindiga sun yi garkuwa da shi
  • Malamin ya kuma yi fatali da labaran da ake yadawa cewa hukumar DSS ta cafke shi inda ya ce babu kamshin gaskiya
  • Sheikh Yabo ya shawarci jama'a musamman malaman addinin musulunci da su rika tabbatar da labari kafin yadawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Malamin Musulunci, Sheikh Bello Yabo ya yi magana kan zargin yan bindiga sun sace shi.

Malamin ya kuma karyata jita-jitar cewa hukumar DSS ta kama shi kamar yadda ake yadawa.

Bello Yabo ya karyata zargin cewa yan bindiga sun sace shi
Sheikh Bello Yabo ya yi magana kan jita-jitar yan bindiga sun sace shi. Hoto: Sheikh Bello Aliyu Yabo.
Asali: Facebook

Bello Yabo ya karyata zargin sace shi

Shehin malamin ya fadi haka ne yayin hira da wakilin Aminiya a yau Talata 10 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki Musulmi ya zabgawa malamin addini mari a bidiyo, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Yabo ya ce mutane da dama suna ta kiransa daga kasashen ketare cewa wai an kama shi.

Malamin ya shawarci al'umma musamman malaman Musulunci su rika tantance bayanai kafin yadawa.

Sheikh Yabo ya ce yana nan lafiya

"Babu dan bindigar da ya yi garkuwa da ni, da farko an ce wai hukumar DSS ta ba da umarnin kama ni."
"Mutane da dama daga nan Sokoto da ma wasu ƙasashe suna ta kira na suna tambaya ta kan gaskiyar maganar an yi garkuwa da ni."
“Yanzu zamani ne na soshiyal midiya inda mutane ke yada bayanai da rade-radi wadanda ba su da tushe."

- Sheikh Bello Yabo

Bello Yabo ya ce yanzu haka da ake hira da shi yana gida tare da iyalansa inda ya tabbatar babu abin da ya same shi.

Bello Yabo ya burgi kirji kan yan bindiga

Kara karanta wannan

"Na yi wasiyya idan an sace ni," Sheikh Bello Yabo ya sha alwashin cafko yan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Bello Yabo ya yi martani kan masu masa gargadi kan yin nasiha ga yan bindiga.

Sheikh Bello Yabo ya ce ko za a dauki ransa ba zai daina magana kan yan bindiga ba saboda hakan ne aikin da Allah ya daura nasa na wa'azi.

Malamin ya bayyana cewa shi sam bai yarda da cewa yan bindiga za su iya galaba a kansa ba har sai sun yi gaba da gaba da miyagun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.