An Shiga Fargaba, Ambaliya Ta Wargaza Maƙabarta a Maiduguri

An Shiga Fargaba, Ambaliya Ta Wargaza Maƙabarta a Maiduguri

  • Al'ummar jihar Borno na cigaba da zama cikin tashin hankali yayin da mummunar ambaliyar ruwa ta kunno kai a Maiduguri
  • Rahotanni sun nuna cewa ruwan ya wargaza maƙabarta bayan shiga gidaje da ma'aikatu da dama da ambaliyar ta yi a safiyar yau
  • Masana lafiya da kungiyoyi sun bukaci daukan matakin gaggawa domin kaucewa hadarin rashin lafiya da rushewar maƙabartar zai jawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Mutane a birnin Maiduguri na fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da aka shafe shekaru ba a gani ba.

An ruwaito cewa ambaliyar ta wargaza wurare da dama ciki har da maƙabarta a birnin Maiduguri.

Ambaliya
Ambaliya ta wargaza makabarta a Maiduguri. Hoto: @nemanigeria
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa masana sun yi kira ga gwamnatin jihar Borno a kan daukan matakin gaggawa kan lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi wa ƴan Najeriya albashir da ASUU ke shirin rufe jami'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwa ya wargaza maƙabarta a Maiduguri

Bayan rusa gidaje da dama, an ruwaito cewa ambaliyar ta wargaza maƙabartar Kiristoci a birnin Maiduguri.

Rahotanni sun nuna cewa maƙabartar na cikin jerin wurare da ruwan ya wargaza a tsohuwar GRA a Maiduguri.

Masana lafiya sun bukaci a dauki mataki

Masana harkar lafiya sun bayyana cewa akwai hadari sosai ganin yadda ruwan ya rusa maƙabarta zai iya tafiya ga gawarwaki kuma zai iya jawo yaduwar cututtuka.

Vanguard ta wallafa cewa kungiyoyin fararen hula sun yi kira domin ɗaukar matakin gaggawa saboda kaucewa yaɗuwar cututtuka.

An fara taimakawa da abinci a Borno

Biyo bayan ambaliyar ruwan, wata kungiyar fararen hula ta fara raba kayan agaji wanda suka hada da abinci ga al'ummar Maiduguri.

Shugaban kungiyar Bulama Abiso ya yi kira ga sauran kungiyoyi da su kawo dauki ga al'umma domin saukaka lamarin.

Kara karanta wannan

'Ku ƙaura,' Gwamnati ta gargaɗi jihohi kan mummunar ambaliya

Ambaliya ta mamaye fadar Shehun Borno

A wani rahoton, kun ji cewa yau aka wayi gari da mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda mutane da dama suka rasa gidaje.

An ruwaito cewa ambaliyar ruwan ta mamaye gidan mai martaba Shehun Borno inda ya fice daga gidan domin neman mafaka a gidan gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng