Sanata Kwankwaso Ya Kadu da Ambaliyar Ruwa a Jihar Borno, Ya Aika Sako

Sanata Kwankwaso Ya Kadu da Ambaliyar Ruwa a Jihar Borno, Ya Aika Sako

  • Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya jajantawa al'ummar Borno kan ambaliyar ruwa da ta mamaye sassan jihar
  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya ga hotuna masu ban tsoro daga Maiduguri, inda ambaliyar ruwa ta mamaye wurare
  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kira ga mahukunta da masu karfin iko da su gaggauta kai dauki ga mutanen da abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Rahotanni daga jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya na nuni da cewa ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Maiduguri a ranar Talata.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya kadu da ganin hotuna na irin barnar da ambaliyar ta yi a jihar ta Borno.

Kara karanta wannan

"Za mu kai dauki Maiduguri": Tinubu ya aika sako ga Zulum bayan ambaliyar ruwa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan ambaliyar ruwa a Maiduguri, jihar Borno
Sanata Kwankwaso ya aika sako ga mahukunta bayan barkewar ambaliya a Borno. Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Facebook

Ambaliyar Borno: Kwankwaso ya magantu

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a safiyar Talata yana mai kira ga mahukunta da masu hannu da shunu da su kai dauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya ce ya ga hotuna masu ban tsoro daga Maiduguri, inda ruwa ya mamaye sassa da dama na birnin.

Kwankwaso ya ce ya na fatan mahukunta da masu hali za su ba da gudunmawa wajen kare rayukan al'umma da garuruwan da abin ya shafa.

Kwankwaso ya aika muhimmin sako

Sakon da Sanata Kwankwaso ya aika na cewa:

"Na ga hotuna masu ban tsoro daga Maiduguri, inda ruwa ya mamaye sassa da dama na birnin.
"Ina kira ga hukumomi da wadanda za su iya taimakawa da su ba da duk wani taimakon da ya dace domin kare al’umma da garuruwansu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da ambaliyar ruwa a Maiduguri, ya ba Shettima sabon umarni

"Hankalinmu ya karkata ga abin da ke faruwa yayin da muke addu'o'i ga gwamnati da al'ummar jihar Borno a wannan mawuyacin lokaci."

Ambaliya ta mamaye gidan sarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa ambaliyar ruwa da ta barke a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta mamaye gidaje a fadar mai martaba Shehun Borno tare da sassan birnin.

Bayan ruwa ya mamaye gidan sarkin, an ce mai martaba Shehun Borno, Alhaji Garba El-Kanemi ya nemi makafa a gidan gwamnatin jihar a halin yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.