Jerin Jihohin da Suka Dage Ranakun Komawa Makarantu da Dalilansu

Jerin Jihohin da Suka Dage Ranakun Komawa Makarantu da Dalilansu

Ɗalibai a makarantun firamare da sakandare a jihohin ƙasar nan sun yi shirin komawa makaranta domin ci gaba da karatunsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Hakan na zuwa ne bayan ƙarewar hutun zangon karatu na 2023/2024 da fara shirye-shiryen tunkarar zangon karatu na 2024/2025.

Kano ta dage ranakun komawa makarantu
Edo da Kano sun dage ranakun komawa makarantu Hoto: @GovernorObaseki, @KyusufAbba
Asali: Twitter

Meyasa jihohi suka ɗage ranakun?

Sai dai, a yayin da wasu jihohin ba su sauya ranakun komawa makarantun ba, wasu sun ɗauki matakin ɗage ranakun da ɗalibai za su koma domin ci gaba da karatunsu.

Wasu daga cikin jihohin da suka ɗauki matakin ɗage komawa makarantun sun danganta hakan ne kan tsadar fetur da ake fama da ita a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kin shiga zanga zanga ya yi riba, gwamna ya ba matasa kyautar N310m

Tsadar fetur ɗin tabbas za ta sanya kuɗaɗen da iyaye suke kashewa wajen zirga-zirgar yaransu zuwa makaranta su ƙaru.

Jihohin da suka ɗage komawa makarantu

Legit Hausa ta tattaro jihohin da suka ɗage komawa makarantu a faɗin Najeriya.

Ga jerinsu a nan ƙasa:

1. Jihar Edo

Gwamnatin jihar Edo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Godwin Obaseki ta ɗage ranakun da ɗalibai za su koma makarantu a faɗin jihar.

Gwamnatin ta ɗage komawa makarantun wanda aka shirya a ranar 9 ga watan Satumban 2024, har sai baba ta gani, cewar rahoton jaridar The Punch.

A sanarwar da babban sakataren ma'aikatar ilmi ta jihar, Ojo Akin-Longe ya fitar, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda wahalar da iyaye za su shiga sakamakon ƙarin kuɗin fetur da aka yi a ƙasar nan.

Matakin da gwamnatin ta ɗauka dai ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

2. Jihar Kano

Kara karanta wannan

A ƙarshe Shugaba Tinubu ya faɗi ayyukan da yake yi da kudin tallafin man fetur

Gwamnatin jihar Kano ta ɗauki matakin ɗage komawa makarantu da aka shirya a ranakun 8 da 9 ga watan Satumban 2024.

A cewar wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilmi, Balarabe Kiru ya fitar, an ɗage komawa makarantun ne har sai baba ta gani, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Daraktan ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda wasu dalilai na gaggawa da suka tilasta yanke hukuncin hakan.

3. Jihar Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin rufe dukkanim makarantun jihar nan take.

Gwamna Zulum ya ɗauki wannan matakin ne domin gujewa rasa rayuka sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnan na jihar Borno ya umurci dukkanin makarantun firamare da sakandare da su rufe, su tafi hutun makonni biyu gabannin ambaliya ta janye.

Kara karanta wannan

An shiga jimami, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu da dama a Arewa

Yunkurin gyara makarantun Kano

A watan Yunin 2024 Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin dawo da martabar ilmi a jihar Kano, ana da labarin nasarorin da aka samu zuwa yanzu.

Gwamnati ta dauki malaman makaranta fiye da 5000 kuma ana gyaran wuraren karatun dalibai, dinka rigunan makaranta da samar da kujeru da tebura.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng