'Yan Kudu da Arewa Sun Hada kai, Sun Tunkari Tinubu kan Tsadar Man Fetur

'Yan Kudu da Arewa Sun Hada kai, Sun Tunkari Tinubu kan Tsadar Man Fetur

  • Karin kudin man fetur a Najeriya na cikin abubuwan da suka cigaba da jan hankulan al'umma saboda wahala da aka shiga
  • Kungiyoyi a Kudu da Arewacin Najeriya sun nuna takaici kan karin kudin man fetur da aka samu a Najeriya a makon da ya wuce
  • Gamayyar kungiyoyin Hausawa, Ibo da kuma Yarabawa sun yi magana da murya daya wajen isar da sako ga shugaba Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyoyi a Najeriya na cigaba da kokawa kan karin kudin man fetur da aka yi a makon da ya wuce.

Kungiyoyin Arewa da Kudu sun buƙaci gwamnatin tarayya ta rage kudin man fetur domin saukakawa al'umma.

Kara karanta wannan

Maganar Sheikh Jingir da wasu abubuwa da suka tayar da kura kan gwamnatin Tinubu

Bola Tinubu
kungiyoyi sun dura kan Tinubu a kan kudin mai. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa wannan ne karon farko da aka samu dukkan kungiyoyin suna magana da murya daya a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar kungiyar Yarabawa kan kudin fetur

Kakakin kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Jayi Ajayi ya ce ana shan wahala da yunwa a mulkin Bola Tinubu.

Jayi Ajayi ya ce tsare tsaren da gwamnatin Bola Tinubu ta fito da su ne suka jefa al'umma cikin wahala da ake fama da ita a Najeriya.

Kungiyar Ibo ta koka kan tsadar fetur

Mai magana da yawun kungiyar Ibo ta Ohanize Ndigbo, Mazi Okechukwu ya ce cire tallafin fetur ya sanya tsare tsaren gwamnati ba su yin fa'ida.

Mazi Okechukwu ya ce cire tallafin man fetur a ba dalibai lamunin karatu tamkar a ba su kudi da hannun dama ne a kwace da hagu.

Kungiyar CNG ta soki tashin kudin fetur

Kara karanta wannan

"Buhari ma ya fi shi": NLC ta fadi gwamnatoci 2 da suka ɗara mulkin Tinubu

Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kungiyar hadin kan kungiyoyin Arewa ta CNG, Jamilu Aliyu Chiranci ya ce gwamnati ba ta jin kukan yan Najeriya.

Jamilu Aliyu Chiranci ya ce sun gargaɗi gwamnati kan karin kudin man fetur amma ta ki sauraren abin da aka fada mata.

Jingir ya yi magana kan kudin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa malamin Musulunci kuma shugaban kungiyar Izala ta res henJos ya yi magana kan karin kudin fetur.

Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya ce masu son bata gwamnatin Musulmi da Musulmi ne suka kara kudin man fetur a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng