DSS Ta Tsorata, Ta Saki Ajaero Mintuna Kafin Wa’adin Kungiyar NLC Ya Cika
- KuMintuna kafin wa'adin da kungiyar NLC ta ba gwamnatin Bola Tinubu ya cika, hukumar DSS ta saki Kwamred Joe Ajaero
- Kungiyar NLC da TUC sun yi barazanar dakatar da komai a kasar wanda suke ganin zai taba tattalin arziki idan ba a sake shi ba
- Hakan ya biyo bayan cafke Ajaero da DSS ta yi a birnin Abuja yana shirin zuwa Landan domin babban taron kungiyar kwadago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar DSS ta sako shugaban kungiyar kwadago, NLC, Kwamred Joe Ajaero da tsakar dare.
Hukumar ta sake shugaban kungiyar ne mintuna kafin wa'adin da NLC ta ba gwamnatin Bola Tinubu ya cika.
DSS ta sake shugaban NLC, Joe Ajaero
Daily Trust ta ce an kama Ajaero ne a jiya Litinin 9 ga watan Satumbar 2024 a filin tashi da saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajaero ya shirya tafiya Burtaniya ne domin halartar wani taro da kungiyar 'yan kasuwar kasar a birnin Landan.
Wani babban ma'aikacin NLC ya tabbatar da sako Ajaero inda ya ce an sake shi ne bisa sharadin beli da aka bayar.
Barazanar da NLC ta yi wa gwamnati
Bayan kama Ajaero ne kungiyoyin NLC da TUC suka yi barazanar dakatar da komai a kasar wanda hakan ka iya shafar tattalin arzikin Najeriya.
Hakan ya biyo bayan shirin NLC domin fara zanga-zanga a kasar idan har gwamnati ba ta sake Ajaero zuwa karfe 12.00 na dare.
Lauyan Ajaero, Maxwell Opara ya ce DSS sun cafke Ajaero duk da sanar da su da ya yi na tafiya zuwa Burtaniya, cewar rahoton Premium Times.
An fadi dalilin kama Ajaero a Abuja
Kun ji cewa rahotanni da suka fito daga wasu jami'an tsaro sun nuna an kama shugaban kwadago ne bisa zargin kin amsa gayyatar 'yan sanda.
Ana hasashen cewa wani kamfanin jigilar jiragen sama ne ya kai Joe Ajaero kara wajen 'yan sandan Najeriya kan wasu abubuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng