TUC Ta Faɗi Hanyar da Za a Sauke Farashin Man Fetur Har Mutane Su Amfana a Najeriya
- Kungiyar TUC ta buƙaci babban banki CBN ya daidaita farashin musayar kuɗi musamman ga kamfanin NNPCL
- Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo ya ce karya darajar Naira ne babban abin da ya jawo tsadar man fetur ba cire tallafi ba
- Osifo ya yi iƙirarin cewa har yanzu kamfanin mai na kasa yana biyan wasu kuɗaden tallafin duk da karin farashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kungiyar kwadago TUC ta ba gwamnatin tarayya shawarar hanyar da za a sauko da farashin man fetur domin saukaƙawa ƴan Najeriya.
TUC ta buƙaci babban bankin Najeriya (CBN) ya tsaida farashin canjin Dala na musamman ga kamfanin mai NNPCL domin kaucewa ƙara jefa mutane cikin wahala.
Shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo ne ya bayyana hakan a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin din Channels ranar Litinin.
TUC ta bada mafita daga tsadar man fetur
Ya ce idan CBN ya ba kamfanin NNPC farashin canjin Dala kamar ₦1000/$ maimakon ₦1,600/$, farashin man fetur zai sauka zuwa N600 daga kusan N900.
Osifo, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar manyan ma’aikatan sashen mai (PENGASSAN), ya ce cire tallafin da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayun 2023 ba shi ne tushen matsalar ba.
A cewarsa karya darajar Naira da wannan gwamnatin ta yi shi ne asalin matsalar da ke sa man fetur ke ƙara tashi.
Osifo ya ce:
"Babbar matsalar ita ce karya darajar Naira wanda ta yi ƙasa daga ₦700/$1 zuwa sama da ₦1,600/$1."
"Idan ku ka ba NNPC farashin canji na musamman, babu bukatar sake biyan wani tallafi. Haka ya dace a yiwa matatar Ɗangote, a tsaida mata farashin sayar da mai.
TUC na zargin ana biyan tallafin fetur
Shugaban na TUC ya ce har yanzu NNPCL na biyan tallafin man fetur duk da ƙara farashin kowace lita daga kusan ₦600 zuwa sama da ₦900.
Festus Osifo ya yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba, illar karin farashin man fetur zai sake jefa mutane cikin ƙuncin rayuwa fiye da halin da ake ciki a baya.
Ya ce TUC za ta kira taro domin tattauna matakin da ya kamata ta ɗauka idan gwamnati ta gaza dawo da farashin mai zuwa kusan ₦600, Tribune ta rahoto.
NNPCL ya ba matatar Ɗangote dama
A.wani rahoton gwamnatin tarayya ta ce matatun man Najeriya ciki har da ta matatar Dangote za su iya sayar da kayayyakinsu kai tsaye ga 'yan kasuwa.
Ta bakin kamfanin man Najeriya (NNPCL), gwamnatin ta ce ko kusa ba ta adawa da matatar Dangote, ko kayyade farashin fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng