Shinkafar Tinubu: Kwankwaso Ya Zargi Gwamnati da Ware Abba cikin Gwamnoni 36

Shinkafar Tinubu: Kwankwaso Ya Zargi Gwamnati da Ware Abba cikin Gwamnoni 36

  • Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya koka kan yadda gwamnatin Bola Tinubu ke ware gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na mika tallafin shinkafar kowace jiha ga gwamnan da ke jagorantarta ne
  • Amma a cewar Kwankwaso, gwamnatin tarayya ta ware Abba Yusuf daga wannan tsari inda aka ba wasu 'yan APC rabon tallafin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya koka kan yadda ya ce gwamnatin Bola Tinubu na nuna wariya ga gwamnan Kano.

Sanata Kwankwaso na zargin gwamnatin Bola Tinubu da ware Abba Kabir Yusuf daga rabon shinkafa da ake bayarwa a matsayin tallafi.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta sanya ranar sake zama da ASUU

Kwankwaso
Kwankwaso ya yi takaicin yadda Tinubu ke nuna wariya ga gwamnan Abba Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce a kowace jiha, gwamna ake ba rabon tallafin shinkafar amma ban da Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya zargi Tinubu da ware Abba

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce mika rabon shinkafa daga gwamnatin tarayya ga jagororin APC a Kano cin fuskar dimokuradiyya ne.

Sanata Kwankwaso ya ce hakan nuna tsantsar wariya ce da kiyayya irinta siyasa, wanda ya ke ganin ba zai kawo ci gaba a kasa ba.

Kwankwaso ya damu kan tsaro a Kano

Jagoran NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya koka kan yadda ya ce gwamnatin tarayya na sauya shugabannin tsaro na fararen kaya (DSS) a Kano.

Kwankwaso ya ce a mako biyu kawai, an sauya shugabannin DSS a Kano har sau uku, lamarin da ya ke ganin matsala ce sosai ga tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Awanni da komawar 'yan Kwankwasiyya APC, gwamnati ta fara rabon shinkafa a Kano

PDP ta fusata kan kalaman Kwankwaso

A baya kun ji cewa jam'iyyar hamayya ta PDP ba ta ji dadin kalaman Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da ya ce shi ne zai yi nasara a zaben 2027 mai zuwa ba.

A kakkausan martanin da PDP ta yi, ta bayyana cewa Kwankwaso dan siyasa ne wanda ba shi da wani tasiri, kuma ya fifita zancen takara kan halin da talaka ke ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.