PDP Ta Fadawa Tinubu Wadanda Suka Dauki Nauyin Zanga Zangar Tsadar Rayuwa
- PDP ta caccaki Bola Tinubu kan cewa wasu yan siyasa ne suka dauki nauyin zanga zangar da aka yi watan Agusta da ta wuce
- Jam'iyyar PDP ta ce abin mamaki ne yadda ake yunwa, amma gwamnatin tarayya na tunanin wasu ne suka dauki nauyin zanga zanga
- Sakataren yada labaran PDP, Debo Olagunagba ne ya yi martani ga Tinubu inda ya ce shugaban kasa ya gaza magance matsalolin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi martani ga gwamnatin tarayya kan zanga zangar tsadar rayuwa.
PDP ta ce abin kunya ne yadda gwamnatin tarayya ta kama yan Najeriya da suka fito zanga zangar tsadar rayuwa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sakataren yada labaran PDP, Debo Olagunagba ne ya yi martani ga gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka dauki nauyin zanga zanga
Debo Olagunagba ya fadawa shugaba Bola Tinubu cewa yunwa da tsadar rayuwa ne suka dauki nauyin zanga zanga a Najeriya.
PDP ta ce har ila yau tsare tsaren gwamnatin Bola Tinubu ne suka jefa al'umma cikin wahalar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.
Yan Najeriya sun yi zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ne a fadin ƙasar nan daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan da ya gabata.
Magana kan kama masu zanga zanga
Jam'iyyar PDP ta ce abin kunya ne yadda gwamnatin Bola Tinubu ta kama wasu masu zanga zangar har ta kai ga kulle su.
Vanguard ta wallafa cewa PDP ta ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta yaki yunwa da tsare tsaren gwamnati suka jawo maimakon kama talakawa.
Debo Olagunagba ya ce akwai bukatar APC ta dauki darasi kan zanga zangar da aka yi wajen magance matsalolin Najeriya.
An koka kan sayen shinkafar Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa a makon da ya wuce gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kaddamar da fara sayar da buhun shinkafa a kan N40,000.
Sai dai yan Najeriya a birnin tarayya Abuja sun koka kan yadda suka gaza gano wajen da gwamnati ke sayar da shinkafar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng