An Samu Asarar Rai bayan Gini Ya Sake Rikitowa a Kano
- Wani mummunan lamari ya afku a jihar Kano, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mace guda, Nafisa Ali da jikkata wasu da dama
- Gini da ya rikito a unguwar Dandago da ke karamar hukumar birni, inda ya danne mutane mutane biyar, yayin da hudu ke asibiti
- Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ta tabbatar da mummunan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Wani gini ya sake faduwa a karamar hukumar birnin jihar Kano yayin da ake ci gaba da samun mamakon ruwan sama a sassan jihar.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa ginin ya rikito a unguwar Dandago tare da danne mazauna gidan.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wata baiwar Allah, Aisha Sani Bala ce ta nemi agajin gaggawa daga hukumar bayan ruftawar ginin.
Kano: Rikitowar gini ya kashe mutum 1
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya shaidawa Legit cewa ginin ya da ruguje ya jawo asarar rai.
Ya bayyana cewa wani mutum guda mai suna Nafisa Ali ta rasu, inda tun da aka ceto ta daga karkashin kasar ba ta cikin hayyacinta.
Gini ya danne mutum 5 a Kano
Kakakin hukumar kashe gobara a Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa ginin da ya rikito ya danne mutane biyar.
Wadanda ginin ya danne sun hada da Nasiru Aliyu mai shekaru 59, Maryam Ali mai shekaru 37, Sadiya Aliy mai shekaru 32, Maimuna Ali mai shekaru takwas da Nafisa Ali.
Kano: Gini ya danne mata da yaranta
A baya mun ruwaito cewa wani gini da ya fado a jihar Kano ya danne wata mata da yaranta, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta yayin da aka mika yaranta asibiti domin samun kulawa.
Mummunan lamarin ya afku ne a unguwar Makwarari da ke jihar Kano a ranar Juma’a, inda ake samun mamakon ruwan sama da ya yi sanadin faduwar ginin da ya kashe matar.
Asali: Legit.ng