'Sai Na yi Gaba da Gaba da Yan Bindiga' Bello Yabo Ya Dauki Zafi bayan Masa Gargadi

'Sai Na yi Gaba da Gaba da Yan Bindiga' Bello Yabo Ya Dauki Zafi bayan Masa Gargadi

  • Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya yi martani kan masu masa gargadi kan yin nasiha ga yan bindiga
  • Sheikh Bello Yabo ya ce ko za a dauki ransa ba zai daina magana kan yan bindiga ba saboda hakan ne aikin da Allah ya daura nasa na wa'azi
  • Malamin ya bayyana cewa shi sam bai yarda da cewa yan bindiga za su iya galaba a kansa ba har sai sun yi gaba da gaba da miyagun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Sheikh Bello Yabo ya yi tsokaci kan gargadi da aka masa a kan daina yin magana a kan yan bindiga.

Kara karanta wannan

"Na yi wasiyya idan an sace ni," Sheikh Bello Yabo ya sha alwashin cafko yan bindiga

Shahararren malamin ya ce yanzu ne ma ya fara nasiha ga yan bindiga domin ko zai rasa rayuwarsa ba zai daina ba.

Bello Yabo
Bello Yabo ya ce zai cigaba da nasiha ga yan bindiga. Hoto: Sheikh Bello Yabo Sokoto
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro abin da Sheikh Bello Yabo ya fada ne a cikin wani bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Yabo zai cigaba da kira ga yan bindiga

Sheikh Bello Yabo ya ce maganar ya dakata da yin nasiha ga yan bindiga masu garkuwa da mutane ba ta taso ba kwata kwata.

Malamin ya ce ko da yana da rayuka 100 ne aka cire 99 saura daya ba zai daina kira zuwa ga yan ta'addan da suke kashe mutane ba.

Sheikh Bello Yabo ya ce ya fi jin tsoron azabar Allah idan ya ɓoye gaskiya a kan ya yi shiru domin jin tsoron azabar yan bindigar Najeriya.

Kara karanta wannan

"Na rasa uwa": Jonathan ya fadi alherin da marigayiya Hajiya Dada ta yi masa

Maganar gaba da gaba da yan bindiga

Sheikh Bello Yabo Sokoto ya ce shi sam bai yarda yan bindiga za su iya galaba a kansa ba har sai ranar da suka yi gaba da gaba tukunna.

Fitaccen malamin ya ce yin gaba da gaba da yan bindiga ne kawai zai nuna cewa yan ta'addar sun fi karfinsa a zahirance.

Sheikh Bello Yabo ya ce kuma a ko da yaushe kofar gidansa a bude take idan akwai wani mugu da yake tunanin far masa.

Yan bindiga sun fara bautar da mutane

A wani rahoton, kun ji cewa al'ummar karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun koka kan yadda yan bindiga suka mayar da su kamar bayi suna yi musu aiki a gona.

Wani mazaunin yankin Allawa ya bayyana yadda yan bindiga da yan ta'adda suka kwace amfanin gona mai tarin yawa hannun mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng