Sojoji Sun Cafke Mata Masu Ba 'Yan Bindiga Bayanai a Jihar Kaduna
- Dakarun sojoji sun samu nasarar kama wasu mata da ake zargin suna haɗa baki da ƴan bindiga a jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin sun cafke matan ne guda biyu bayan sun je siyo kayayyaki ga ƴan bindiga a ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar
- Dakarun sojojin sun yi nasarar cafke matan ne bayan sun samu bayanan sirri a kansu sannnan suka biyo sawunsu zuwa kasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Dakarun sojoji sun kama wasu mata guda biyu da ake zargin masu ba ƴan bindiga bayanai ne a jihar Kaduna.
Sojojin sun cafke matan ne da ake zargin suna haɗa baki da ƴan bindiga a ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ce wani shugaban al’umma da ya so a sakaya sunansa ya bayyana hakan ga wakilinta ta wayar tarho a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun cafke masu haɗa baki da ƴan bindiga
Ya ce sojoji daga Katari sun bi sawun waɗanda ake zargin ne a ranar Laraba bayan bayanan sirri da suka samu cewa sun je kasuwar ƙauyen SCC domin siyo kayan abinci da sauran kayayyaki ga ƴan bindigan.
Shugaban al'ummar ya ce tun da farko ƴan banga sun yi yunƙurin cafke waɗanda ake zargin sati biyu da suka wuce a kasuwar Kagarko amma sai suka tsere.
Wani ɗan banga a yankin, mai suna Shehu, ya tabbatar da kamun da aka yi wa waɗanda ake zargin.
"Eh, sojoji ne suka kama matan guda biyu a ƙasuwar ƙauyen SCC ranar Laraba."
- Shehu
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai ce uffan ba kan lamarin.
Sheikh Gumi ya magantu kan ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana kan matsalar ƴan bindiga da ake fama da ita.
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ƴan siyasa ba sa ɗaukar nauyin tashe-tashen hankula a yankin Arewacin ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng