Gwamnatin Jiha a Arewa Ta Kulle Kamfanonin Tsohon Gwamna, Ta Jero Hujjoji

Gwamnatin Jiha a Arewa Ta Kulle Kamfanonin Tsohon Gwamna, Ta Jero Hujjoji

  • Gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanin tsohon gwamna, Samuel Ortom kam zargin kin biyan haraji na makudan kudi
  • Ana zargin kamfanin mai suna Oracle Business mallakin tsohon gwamna, Ortom da kin biyan haraji har N93.5m
  • Sai dai wasu na ganin hakan bita da kullin siyasa ne da ake yi domin kassara harkokin kasuwancin Ortom a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Hukumar tattara kudaden shiga a jihar Benue ta kulle kamfanin tsohon gwamna, Samuel Ortom.

Hukumar ta dauki matakin ne saboda kin biyan haraji da kamfanin ya ki biya har na N93.5 da ake zargi.

Gwamnatin jiha ta kulle kamfanonin tsohon gwamna kan haraji
Gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanonin tsohon gwamna, Samuel Ortom kan kin biyan haraji. Hoto: Alia Hyacinth, Samuel Ortom.
Asali: Facebook

Benue: An rufe kamfanonin tsohon gwamna, Ortom

Kara karanta wannan

"Ku taimake mu": Gwamna a Arewa ya sallami shugabannin kananan hukumomi 17

Punch ta ruwaito cewa mukaddashin shugaban hukumar, Sunday Odagba shi ya jagoranci samamen a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin mai suna Oracle Business yana da rassa daban-daban da ke gudanar da kasuwanci mallakin Samuel Ortom.

Wata kungiya da ke tare da Ortom ta zargi Gwamna Alia Hyacinth da neman kassara harkokin kasuwancin tsohon gwamnan.

Shugaban kungiyar, Amos Uchiv shi ya yi wannan zargi a yau Lahadi 8 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Thisday.

Uchiv ya ce akwai alamun tambayoyi kan yadda aka sako harkokin kasuwancin Ortom a gaba wanda da sanin gwamnan ake yi.

Gwamnatin Benue ta ƙaryata zarginta da ake

Sai dai hadimin Gwamna Alia, Solomon Iorpev ya ce gwamnatin jihar ba ta damu ba domin kokarin neman kudin jihar da aka karkatar.

Har ila yau, babban daraktan kamfanin, Chris Omiyi ya ce sun samu rahoton kan biyan harajin N138m yayin da suka yi korafi aka rage zuwa N38m inda ya ce duk da haka ya yi yawa.

Kara karanta wannan

'Ba za mu iya rayuwa haka ba' An hada kai, an yi rubdugu ga Tinubu kan kudin mai

Kotu ta ba Gwamna Alia damar binciken Ortom

Kun ji cewa yayin da ake cigaba da shari'a tsakanin Gwamna Alia Hyacinth da Samuel Ortom, kotu ta yi zama kan matsalarsu tare da yanke hukunci.

Babbar Kotun jihar da ke birnin Makurdi ta yi fatali da korafe-korafen Ortom da ke kalubalantar Hyacinth kan bincikensa.

Hakan na zuwa ne bayan Hyacinth ya kafa kwamitin binciken gwamnatin da ta shude game da zargin badakala a watan Faburairun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.