A Karon Farko, Basarake daga Arewa Ya Yi Mubaya'a ga Sanusi II, Ya Roke Shi Alfarma
- Sarkin Potiskum da ke jihar Yobe, Umar Bauya ya kai ziyarar goyon baya ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
- Basaraken ya ce ya zo fadar Sanusi II ne domin yin mubaya'a da nuna goyon baya a gare shi da mutanensa baki daya
- Sarkin ya roki Sanusi II da ya ba da gudunmawarsa wurin karasa gina masallacin Juma'a da suka faro shekarun baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karbi bakwancin fitaccen basarake a fadarsa.
Sarkin Potiskum da ke jihar Yobe, Mai Martaba Umar Bauya shi ya kai ziyarar goyon baya ga Sanusi II.
Kano: Sanusi II ya karbi Sarkin Potiskum
Shafin Sanusi II Dynasty ya ruwaito a Facebook cewa wannan shi ne karon farko da basarake daga Arewa ya kawo ziyarar goyon baya ga Sanusi II.
Mai Martaba, Bauya ya samu tarba mai kyau daga Sanusi II da kuma sauran sarakunan gargajiya daga jihar Kano.
Sarkin ya ce ya zo fadar Sanusi II domin yin mubaya'a a matsayinsa na Sarkin Kano da kuma Khalifan Tijjaniya.
Basaraken ya tunatarwa Sanusi II cewa tarihi yana maimaita kansa bayan dawowarsa karaga inda ya ce hakan ya faru da shi shekarun baya.
Sarkin Potiskum ya roki alfarmar Sanusi II
"Hakan ya faru da ni shekaru 26 da suka wuce, amma da taimakon Allah na dawo karaga kuma ina zaman lafiya da al'umma ta."
"Dawowar Sanusi II ya nuna cewa basaraken ya damu da bukatun al'umma ne, saboda haka ni da mutane na muna goyon bayansa."
- Umar Bauya
Basaraken har ila yau, ya roki Sanusi II taimakon karasa ginin masallacin Juma'a da suka fara shekarun baya amma ba su iya karasawa ba.
Sanusi II ya jajanta rasuwar Hajiya Dada
Mun baku labarin cewa yayin da ake jimamin rasuwar mahaifyar Umaru Musa Yar'Adua, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya je ta'aziyya.
Mai martaban ya isa jihar Katsina ne domin yin ta'aziyya ga iyalan marigayiyar inda ya ce tabbas an yi babban rashin uwa mai dattaku.
Asali: Legit.ng