Babban Alkali Ya Kubuta daga Hannun 'Yan Ta'adda Bayan Kwashe Watanni a Tsare
- Mai shari'a Haruna Mshelia wanda ake tunanin ƴan ta'addan Boko Haram ne suka sace shi ya shaƙi iskar ƴanci
- Alƙalin na babbar kotun jihar Borno ya kuɓuta ne a ranar Asabar, 7 ga watan Satumban 2024 bayan ya kwashe watanni biyu a tsare a hannun miyagun
- Sai dai, matar alƙalin da direbansa waɗanda aka yi garkuwa da su a tare suna ci gaba da zama a tsare a hannun ƴan ta'addan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Alƙalin babbar kotun jihar Borno, Haruna Mshelia, wanda aka yi garkuwa da shi ya kuɓuta.
Wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne suka yi garkuwa da Haruna Msheila a ranar 24 ga watan Yuni.
An sace alƙalin tare da iyalansa
Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa waɗanda suka yi garkuwa da shi sun sake shi ranar Asabar, 7 ga watan Satumban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi garkuwa da shi ne yayin da yake tafiya daga garin Biu zuwa Maiduguri tare da matarsa, direban sa, da wani jami'in ɗan sanda.
Harin wanda ya auku a tsakanin Buratai da ƙauyen Gujba, ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an ɗan sandan.
Alƙali ya kuɓuta a Borno
Jaridar Leadership ta ce an sanar da sakin alƙalin ne a dandalin WhatsApp na lauyoyin Borno.
Saƙon na cewa:
"Alhamdulillah, mun samu labarin sakin mai shari’a Haruna Mshelia."
Sanarwar ta ce Haruna Mshelia ne kawai aka saki. Matarsa da direbansa suna ci gaba da zama a tsare a hannun miyagun.
Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) reshen jihar Borno, Hamza Zannah ya tabbatar da kuɓutar alƙalin.
Bello Turji ya sa haraji a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa mazauna kauyen Moriki da ke Zamfara sun shiga tashin hankali tun bayan da aka rahoto cewa jami'an sojojin da aka girke a kauyen sun kashe shanun Bello Turji.
An ce sabon kwamandan rundunar sojin da aka girke a kauyen Moriki ne ya kashe shanun Bello Turji, lamarin da dan ta'addan ya ce ba zai lamunta ba.
Asali: Legit.ng