An Shiga Tashin Hankali a Jhar Neja: Mutane 30 Sun Mutu a Fashewar Tankar Mai

An Shiga Tashin Hankali a Jhar Neja: Mutane 30 Sun Mutu a Fashewar Tankar Mai

  • Fashewar wata tankar mai ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 30 a hanyar Agaie-Bida a jihar Neja da misalin 12:30 na ranar Lahadi
  • Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) Abdullahi Baba-Arab ne ya bayyana hakan sanarwar da ya fitar
  • NSEMA ta bayyana cewa tankar man ta yi karo ne da wata tirela dauke da shanu da mutane, lamarin da ya jawo babbakewar mutane da shanu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Sama da mutane 30 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon fashewar tankar mai a karamar hukumar Agaie ta jihar Neja.

An bayyana cewa tankar man ta yi karo ne da wata motar tirela dauke da matafiya da shanu daga karamar hukumar Wudil ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke budurwar wani rikakken ɗan bindiga a Taraba, bayanai sun fito

Hukumar NSEMA ta yi magana kan hatsarin tankar man da tireba a Neja, mutane 30 sun mutu
Neja: Sama da mutane 30 da shanu 50 suka mutu nan take a fashewar tankar mai. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Tanka ta fashe, mutane sun mutu

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) Abdullahi Baba-Arab ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wata sanarwa, inji rahoton The Punch.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 12:30 na rana a kan titin Lapai-Agaie mai nisan kilomita 2 daga yankin Dendo a karamar hukumar Agaie.

A cewar Baba-Arab, sama da shanu 50 ne suka babbake da ransu yayin da wasu motoci guda biyu; babbar motar daukar karafuna da wata motar daukar kaya suka kone a cikin gobarar.

NSEMA ta yi bayanin iftila'in

Sanarwar ta NSEMA ta ce:

“NSEMA ta samu rahoton fashewar wata tankar mai a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024 da misalin karfe 12:30 na rana a kan titint Lapai-Agaie, kilomita 2 daga Dendo a Agaie.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta dage ranakun komawa makaranta, ta fadi dalili

“Lamarin ya faru ne a lokacin da wata tankar fetur ta yi karo da wata motar tirela da ke dauke da matafiya da shanu daga Wudil a jihar Kano da ke kan hanyar zuwa Legas.
“Sama da mutane 30 ne aka tabbatar sun mutu, tare da babbakewar shanu sama da 50 da ransu. Har yanzu tawagar NSEMA tare da haɗin gwiwar LGEMCs suna wurin da abin ya faru."

Ribas: Tankokin mai sun fashe

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla motoci 100 da mutane masu yawa ne suka kone yayin da wasu tankokin fetur suka fashe a karamar hukumar Eleme a jihar Ribas.

An tattaro cewa lamarin ya fara ne lokacin da wata tanka maƙare da man fetur ta fashe kuma wutat ta bazu zuwa wasu tankokin da suka maƙale a cinkoso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.