SERAP: An Ba Tinubu Wa'adin Awa 48 Ya Janye Karin Kudin Fetur, Ya Binciki NNPCL
- Kungiyar SERAP ta ba Shugaba Bola Tinubu wa'adin awanni 48 da ya umarci kamfanin NNPCL ya gaggauta janye karin kudin man fetur da ya yi
- Bayan bukatar janye karin kudin man, SERAP ta kuma bukaci Shuga Tinubu da ya ba ministan shari'a da hukumomi umarnin bincikar NNPCL
- Abubakar Sani da Malam Bashir sun koka kan yadda karin kudin fetur ya shafi rayuwarsu da kuma dawainiya da iyalansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya umurci kamfanin NNPCL ya gaggauta janye karin kudin fetur.
A wata wasika mai kwanan wata 7 ga Satumba 2024 daga mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ta yi ikirarin cewa karin kudin man ya sabawa ka’ida.
A wasikar da ta wallafa a shafinta na intanet, SERAP ta ce karin kudin man ya take wani bangare na kundin tsarin mulki da kuma hakkokin bi Adama na kasa da kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SERAP ta soki karin kudin fetur
SERAP ta bukaci shugaban kasar da ya yi amfani da karfin ikonsa domin"ya umarci kamfanin NNPCL ya janye wannan karin man da ya yi wanda ya saba doka da tsari."
"An dade ana takewa 'yan Najeriya 'yancinsu da kuma hana su sanin dalilin da ya sa suke ci gaba da biyan kudaden almundahana a bangaren mai.
“Ƙarin farashin man fetur ya kara jefa ‘yan ƙasa cikin mawuyacin hali wadanda dama can suna fama da talauci ba tare da iya biyan buƙatun su na rayuwa ba.
“Kara fashin bai zama dole ba, domin ya samo asali ne daga gazawar gwamnatocin da suka shude wajen magance zarge-zargen cin hanci da rashawa a bangaren mai."
- A cewar SERAP.
SERAP na so a binciki NNPCL
SERAP ta kuma bukaci Tinubu da ya umarci ministan shari’a, Lateef Fagbemi da hukumomin yaki da rashawa da su binciki zargin cin hanci da rashawa a cikin kamfanin NNPC.
“Cin hanci da rashawa a bangaren mai tare da rashin gaskiya da rikon amana wajen amfani da kudaden gwamnati a ayyukan NNPC, ya haifar da kara kudin mai ba bisa ka’ida ba.
“Tuhuma da bincikar kamfanin mai na NNPC kan zargin laifuffukan cin hanci da rashawa a bangaren mai zai zama biyan bukatar 'yan kasar.
Mun damu kwarai da yadda tattalin arzikin Najeriya ke kara tabarbarewa, wanda karin farashin man fetur zai kara jefa mutane cikin talauci."
'Yan kasa na kukan tsadar mai
A zantawarmu da Abubakar Sani, wani mai tuka adaidaita sahu a Kaduna, ya ce karin kudin man fetur ya jefa sana'arsa a gariri domin yanzu ba zai iya hada 'balance' ba.
'Balance' a wajen masu adaidaita sahu wata kalma ce da ke bayyana kudin da suke ajiyewa wadanda suka karbi hayar babur a wajensu a tsarin biyan mako, ko wata.
Abubakar Sani ya ce yana ajiye N8,000 duk mako, amma sakamakon karin kudin fetur din, hakan ba zai taba yiyuwa ba, ko da kuwa za su yi karin kudin zirga zirgar.
Wani Malam Bashir, wanda magidanci ne ya ce yana da yakinin nan da mako daya kayan abinci za su iya kara kudi, abin da ke faruwa kenan a duk lokacin da aka yi karin kudin fetur
Malam Bashir ya ce su masu mata fiye da biyu sun dade suna kwana ba a dora girki ba, sai an samu sa'a a kwadago ne ake iya dafa shinkafa ko kuma a sha garin rogo.
Yarabawa sun soki karin kudin fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar dattawan Yarabawa sun nuna adawa da matakin kamfanin NNPCL na kara kudin man fetur zuwa sama da N855 a fadin kasar.
Kungiyar ta nemi Shugaban kasa Bola Tinubu da ya duba halin da 'yan kasar za su sake shiga sakamakon wannan karin kudin man, inda Yarabawan suka nemi a janye karin.
Asali: Legit.ng