Sharudan NNPCL Ka Iya Kawo Cikas ga Matatar Dangote bayan Kara Kudin Mai
- Kamfanin mai na NNPCL ya fadi sharadin daukar kaya daga matatar man Aliko Dangote a Najeriya yayin da ake tsadar mai
- Kamfanin ya ce zai sayi kayan ne kawai idan farashin man Dangote ya fi na kasuwar duniya araha a halin da ake ciki
- Wannan na zuwa ne bayan matatar man Dangote ta bayyana cewa tana jiran kamfanin NNPCL ne ya fara daukar kayanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Da alamu matatar Aliko Dangote za ta fara fitar da mai ketare saboda sharudan kamfanin NNPCL.
A baya, matatar ta ce tana jiran kamfanin ne ya fara daukar kayanta a kasar saboda samun wadatar mai.
NNPCL ya fadi sharadin daukar man Dangote
Sai dai NNPCL ya ce zai sayi man Dangote ne idan ya fi farashin kasuwar duniya araha, kamar yadda ya ruwaito a shafinsa.
Kakakin kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye shi ya tabbatar da haka a jiya Asabar 7 ga watan Satumbar 2024.
Kamfanin ya ce zai dauki kayan ne kawai idan har farashin fetur ya fi na matatar Dangote tsada a Najeriya.
Ya ce Dangote da sauran matatun mai suna da damar siyar da kayansu ga duk yan kasuwa da ke bukata.
Har ila yau, kamfanin ya ce ba shi da wani shiri na zama mai raba kaya ga yan kasuwa ko masu bukata a irin wannan yanayi.
MURIC ta zargi NNPCL da dakile Dangote
Wannan martani na zuwa ne bayan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta zargi NNPCL da yi wa Dangote makarkashiya.
MURIC ya ce karin farashin mai a daidai wannan lokaci zai hana matatar Dangote samar da man cikin farashi mai rahusa.
Legit Hausa ya ji ta bakin wani mai siyar da mai da ya bayyana sunansa da Abdullahi Jalo a Gombe.
Abdullahi ya ce matakin kamfanin NNPCL ka iya kara farashin mai musamman idan matatar Dangote ta fara fitarwa ketare.
"Siyan mai daga matatar zai iya fin sauki fiye da fita ketare wanda hakan zai kara farashin ne kawai."
- Abdullahi Jalo
Hasashen farashin mai a matatar Dangote
Kun ji cewa wani masanin harkokin mai a Najeriya, Henry Adigun ya yi fashin baki kan farashin da matatar Dangote za ta tsaida.
Adigun ya ce ba zai taba yiwuwa Dangote ya siyar a farashi kasa da na kamfanin NNPCL ba saboda ana lissafi da dala ne.
Mai fashin bakin ya kuma ce man Dangote shi ne mafi kyau a duniya domin haka duk abin da yake da kyau zai yi tsada.
Asali: Legit.ng